'Na Samu Lafiya,' Buhari Ya Fadi Kalubalen da Ya Fuskanta a Lokacin Mulkinsa

'Na Samu Lafiya,' Buhari Ya Fadi Kalubalen da Ya Fuskanta a Lokacin Mulkinsa

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mulkin Najeriya abu ne mai wahala saboda kalubalen da ke tattare da kasar
  • Muhammadu Buhari ya ce yana samun lafiyar jiki fiye da lokacin da yake kan mulki, kuma ya yi kira ga shugabanni da su ji tsoron Allah
  • Buhari ya yi magana ne a taron shugabannin APC a Katsina inda aka tattauna shirye-shiryen zaben kananan hukumomi na watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mulkin Najeriya na tattare da kalubale masu yawa.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa shugabanci na sanya wa shugabanni fuskantar matsaloli da suka shafi tafiyar da al’amuran kasa.

Buhari
Buhari ya ce akwai wahala a jagorancin Najeriya. Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa Buhari ya yi wannan bayanin ne a wurin wani taron shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa taron ya gudana ne domin shirye-shiryen zaben kananan hukumomi da aka shirya yi a ranar 15 ga Fabrairu, 2025 a jihar.

Buhari ya fadi kalubalen mulki a Najeriya

Da yake nazarin mulkinsa, shugaba Buhari ya ce duk da irin kokarin da ya yi wajen magance matsalolin kasar, sau da dama yana fuskantar suka daga jama’a.

Tsohon shugaban kasar ya ce ya ce:

"Mutanen da ba su cikin gwamnatin kasar nan ba su fahimtar yadda abubuwa suke da wahala wajen tafiyar da Najeriya."

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa tun bayan da ya mika mulki ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Mayu 2023, lafiyarsa ta inganta sosai.

A cewar Muhammadu Buhari;

"Mutanen da suke zuwa wurina sun ce na fi kyau a yanzu fiye da lokacin da nake ofis."

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi fama da rashin lafiya mai tsanani a lokacin wa'adin mulkinsa na farko.

Kara karanta wannan

Rikicin Tinubu da gwamnan Bauchi: Minista ya fadi dalilin rashin jituwa

Rashin lafiyar ta sanya tsohon shugaban kasar tarewa a asibiti a birnin London na tsawon lokaci kafin ya samu lafiya.

Kiran Buhari ga shugabanni a Najeriya

Buhari ya yi kira ga shugabannin siyasa da su ji tsoron Allah wajen tafiyar da dukiyar jama’a da kuma gudanar da mulki.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa gaskiya da amana ne kawai za su ceto Najeriya daga matsalolin da take ciki.

"Abin da Najeriya ke bukata shi ne shugabanni masu tsoron Allah da kuma gaskiya wajen gudanar da dukiyar al’umma."

- Shugaba Muhammadu Buhari

Shirye-shiryen zabe a Katsina

Taron da Buhari ya halarta ya mayar da hankali kan shirye-shiryen zaben kananan hukumomi da za a yi a watan Fabrairu a Katsina.

A wurin taron, gwamna Dikko Umar Radda ya yi bayani kan shirye-shiryen da gwamnatinsa ke yi domin ganin an gudanar da sahihin zabe.

Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar Katsina, Aminu Bello Masari da Ibrahim Shehu Shema.

Kara karanta wannan

'Buhari ya nuna rashin gamsuwa da mulkin Bola Tinubu,' PDP ta tono magana

Jam'iyyar APC ta sha alwashin lashe zaben kananan hukumomi a jihar, ta ce mutane za su zabe ta saboda ayyukan da Dikko Radda ke yi.

Gwamna Radda ya mika Katsina ga PDP

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kastin, Dikko Umaru Radda ya yi kuskure a yayin yakin neman zaben kananan hukumomi.

Dikko Radda ya bayyana kuskuren kiran PDP maimakon APC a matsayin gazawa irinta dan Adam wanda kowa zai iya yi a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng