Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

  • Wata maijego mai suna Nizi Rozay, ta samu kyautar dankareriyar mota kirar Range Rover 2023 daga mijinta a matsayin kyautar nakuda bayan haihuwar dansu
  • Maijegon wacce ke da yara uku ta je shafinta na Twitter don wallafa hotunan dankareriyar motar, kuma tuni suka yadu
  • Mabiya shafukan nata wadanda suka ga hotunan sun je sashin sharhi don tayata murna

Wata matar aure ta yi nakuda mai tsada bayan maigidanta ya siya mata dankareriyar mota kirar Range Rover 2023 a matsayin tukwicin haifa masa da na uku.

Nizi Rozay ta bayyana cewa sun yi odar tsadaddiyar motar a watan Janairu yayin da ta wallafa hadaddun hotunan dankarariyar abar hawan a shafinta na soshiyal midiya, kuma tuni suka yadu.

Mace da mota
Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da Hoto: @MissNizi/Evgeniia Siiankovskaia
Asali: Twitter

Ta wallafa hadaddun hotuna hudu masu sace zuciyar duk wanda ya yi arba da su dauke da rubutu kamar haka:

Kara karanta wannan

Dan kasuwa ya toshe al'aurarsa saboda bai san ya sake haihuwa saboda tsadar kudin makaranta 'yayansa 5

“A karshe na karbi tukwicin nakudata! Musamman muka yi odarta a watan Janairu kuma a karshe ta zama tawa! Sabuwar Range Rover kirar 2023” ta rubuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin mutane a kasa:

@ethereal_aura5 ta ce:

“Na taya ki murna yarinya! Shin tukwicin nakuda na goyon ciki? Ya zama sabon abu a gareni.”

@MissNizi ta amsa

“Kwarai! Allah ya azurtani da mijina da samun sabon da! Muna da yara uku a yanzu kuma sabon jinjirin shine na karshe da za mu haifa don haka wannan kyautar na “nakudar” karshe ce.”

@Nature67308884 ta ce:

“Da kin zaba wata kalar ba baka ba, amma dai na tayaki murna.”

@sanjeeva7 ta ce:

“Na taya ki murna a kan motar da za ta shafe rabin lokaci a gareji.”

@MissNizi ta yi martani:

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

“Wannan ita ce Range Rover ta ta hudu kuma ban taba saka kowannensu a gareji ba. Don haka ina tayaki murna da kasancewarki mai bahaguwar tunani.”

Bidiyon Yadda Lakcara Ta Taya Dalibarta Rainon Jinjirinta Yayin da Take Rubuta Jarrabawa

A wani labarin, wata lakcara da ke sanya idanu kan yadda ake gudanar da jarrabawa ta nuna karamci sosai bayan ta taya wata dalibarta da ke zana jarrabawa kula da jinjirinta.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano lakcarar tana rainon jinjirin dalibar tata cikin yanayi mai ban tausayi.

A cikin dan gajeren bidiyon wanda aka daura a TikTok, an gano lackarar tana zagaye dakin jarrabawar dauke da jinjirin a hannunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel