Ta zub da hawayen farin ciki yayinda mijinta yayi mata kyautar Tsaleliyar mota Venza matsayin tukwicin nakuda

Ta zub da hawayen farin ciki yayinda mijinta yayi mata kyautar Tsaleliyar mota Venza matsayin tukwicin nakuda

  • Mijin wata 'yar Najeriya da ta haifi da namiji kwanan nan ya gwangwaje ta da dalleliyar mota kirar Venza
  • A cikin bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta, ana iya ganin matar cikin hawayen farin ciki yayin da take rawa da mijinta
  • Matar ta ci gaba da share hawayenta yayin da tarin makaɗa ke nishadantar da ita, mijinta da mutanen da suka hadu don taya su murna

Wani bidiyo mai kayatarwa ya burge jama’a inda wata 'yar Najeriya ta fashe da hawayen farin ciki bayan mijinta ya yi mata kyautar mota kirar Vanza a matsayin tukwicin haifa masa ‘da namiji.

A bidiyon da @sikiru_akinola ya yada a shafin Instagram, an gano matar da mijinta suna rawa yayin da yayi mata jagora zuwa wajen motar.

Bidiyon uwargida da ta fashe da kuka yayin da mijinta ya yi mata kyautar Venza tukwicin haifa masa ‘da
Bidiyon uwargida da ta fashe da kuka yayin da mijinta ya yi mata kyautar Venza tukwicin haifa masa ‘da Hoto: @sikiru_akinola
Asali: Instagram

A cewar @sikiru_akinola, kyautar ta zo kwanaki hudu bayan matar ta haifi ‘da namiji.

Kara karanta wannan

A tura matasan NYSC faggen yaki da yan bindiga, wanda ba zai je ba a daina biyansa albashi

@sikiru_akinola ya rubuta:

"Jiya, yayana kuma Shugaban @imageplusfotography, Daud Oreoluwa Balogun ya yi wa matarsa bazata da Venza. Wannan ya zo kwanaki hudu bayan isowar ɗan nasu."

Ana iya ganin masu taya murna suna ɗaukar bidiyon maijegon yayin da makaɗa ke nishadantar da kowa.

An yi martani kan bidiyon

Da yake mayar da martani, wani mai amfani da Instagram mai suna@kmaxxofficial ya ce:

"Awwwww, wannan yayi kyau."

Miji ya maka matarsa a kotu bisa ɗaukar cikin wani gardi duk da igiyar aurensa na kan ta

A wani labarin, wata kotun gargajiya da ke jihar Legas, a ranar Alhamis, ta amince Akinola Ikudola dan kasuwa mai shekaru 65 ya rabu da matarsa Funsho bisa zargin ta da kunso ma sa cikin wani duk da igiyar auren sa na kan ta.

Kara karanta wannan

Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, ya ce ya kamata a raba auren tunda sun gaji da zama da juna a matsayin miji da mata.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, alkali ya ba matar damar rike yaran su kuma ya bai wa Akinola umarnin biyan ta N10,000 duk wata don ciyar da su tare da wajabta ma sa ilimin yaran da walwalar su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel