"Matata Ta Fara Mani Wani Abu Saboda Bana Gamsar da Ita a Gadon Aure," Miji Ya Kai Ƙara Kotu

"Matata Ta Fara Mani Wani Abu Saboda Bana Gamsar da Ita a Gadon Aure," Miji Ya Kai Ƙara Kotu

  • Abin mamaki baya karewa yayin da wani magidanci ya nemi kotu ta raba aurensa saboda ba ya gamsar da matarsa a lokacin saduwa
  • Dennis Sikanika ya ce matar ta ɗauki hakan a matsayin wani babban al'amari har ta fara masa barazanar kisa saboda rashin ƙoƙarinsa
  • Ya shaida wa alƙalin kotun yanki cewa tun kafin a ɗaura masu aure ya faɗawa matar cewa shi rago ne a harkokin kwanciyar aure

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zambia - Idan da ranka za ka sha kallo, wasu ma'aurata sun gurfana gaban alƙali saboda mijin ba ya iya gamsar da matar a wurin saduwar aure a kasar Zambia.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya kai ga matar ƴar kimanin shekara 32 a duniya, Faustina Chola ta fara barazanar kashe mijin matuƙar bai ƙara dagewa a gado ba.

Kara karanta wannan

"Yana da ɗaure kai," Falana ya faɗi kuskuren da aka yi a hukuncin shari'ar sarautar Kano

Gudumar kotu.
Magidanci ya nemi alkali ya raba aurensa saboda matar tana masa barazana Hoto: Court of appeal
Asali: Twitter

A rahoton da jaiƙridar Zambia Observer ta tattaro, wannan ya sa magidancin ɗan shekara 49 a duniya, Dennis Sikanika, ya maka matarsa a gaban kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya roƙi ƙaramar kotun yanki da ke zamanta a Lusaka Matero, ƙasar Zambia ta taimaka ta kashe wannan aure tun kafin mai ɗakinsa ta zama ajalinsa.

Meyasa ya kai lamarin kotu?

Da yake jawabi a kotun, Mista Sinkala ya bayyana mamakinsa kan yadda matarsa ta ɗauki lamarin rashin gamsar da ita da girma har take masa barazana.

A cewarsa, ko kaɗan bai cuce ta ba domin tun kafin su yi aure a 2014 ya faɗa mata cewa shi rago ne a ɓangaren kwanciya, ba ya iya sauke nauyin namiji 100%.

Duba da wannan barazana, magidancin ya garzaya yana neman alkali ya shiga tsakani, ya raba auren kowa ya kama gabansa tun kafin ta aikata nufinta, cewar Tribune Nigeria.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir ya faɗi matakin da ya ɗauka kan hukuncin soke naɗin Sanusi II

Lauya ta yi wuff da mijin wata mata

A wani rahoton kun ji cewa Wata bazawara ta shiga damuwa bayan ta gano tsohon mijinta da ya sake ta ya auri lauyanta bayan gama shari'a a kotu

Lauyar ita ce ta wakilce matar a yayin da take neman saki a wajen tsohon mijinta a kotu, sannan bayan ƴan makonni ta yi wuff da shi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262