Zanga Zanga Ta Barke a Isra’ila kan Kin Jinin Netanyahu da Yakin Iran
- Yan Isra’ilada dama sun gudanar da zanga-zanga a Tel Aviv domin nuna adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu a kasar
- Wani dattijo mai shekaru 83 mai suna David Alkan ya bayyana cewa rabuwar kawuna a cikin Isra’ila ta fi zama barazana ga kasar fiye da Iran
- Masu zanga-zangar sun rika dauke da alluna masu rubuce-rubuce kamar “Dakatar da kisan kare dangi” da “Bibi Escobar” domin sukar Netanyahu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Dubban Isra’ilawa sun fito zanga-zanga a birnin Tel Aviv cikin dare domin nuna rashin amincewa da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun koka kan hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kudancin Lebanon da kuma yakin Iran.

Source: Facebook
Musabbabin zanga-zanga a Isra'ila
Rahotanni sun bayyana cewa zanga-zangar ta biyo bayan karuwar rikice-rikice da rashin jituwar siyasa a cikin Isra’ila dangane da yakin Iran da Lebanon, cewar Middle East Eye.
Sun kuma koka kan takaddama kan batun kebance wasu Yahudawan daga aikin soja gabanin zabukan gama gari da ake sa ran gudanarwa daga baya a shekarar nan.
Wani dattijo mai shekaru 83 mai ritaya, David Alkan, ya bayyana cewa ya halarci zanga-zangar ne domin nuna adawa da gwamnatin da ya bayyana a matsayin bala’i ga kasar.
Ya ce gwamnatin Netanyahu tana yaudarar jama’a ta hanyar yada labaran karya da bayanan da ba su dace ba, yana mai cewa hakan na kara haddasa rabuwar kawuna a cikin al’umma.
Alkan ya kara da cewa a ganinsa, rikicin cikin gida da rashin hadin kai a Isra’ila sun fi zama babban barazana ga kasar fiye da Iran.

Source: Getty Images
Abin da masu zanga-zanga ke cewa
Bidiyon da aka wallafa daga wajen zanga-zangar ya nuna masu zanga-zangar na dauke da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban da suka hada da “Dakatar da kisan kare dangi” da kuma “Manta da ranar 7 ga Oktoba.”
Wasu kuma sun dauki alluna masu dauke da kalmar “Bibi Escobar,” wacce ke kwatanta lakabin Netanyahu da sunan fitaccen dan safarar miyagun kwayoyi na Colombia, Pablo Escobar, cewar Times of Israel.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa suna bukatar gwamnati ta sauya manufofinta kan yakin Lebanon tare da magance matsalolin cikin gida da ke kara rarraba al’ummar Isra’ila.
An yi zanga-zanga a Isra'ila
A baya ma, kun ji cewa an gudanar da wata karamar zanga-zangar ƙin jinin yaƙi a Tel Aviv inda mutane suka yi kira ga Isra'ila ta janye daga harin da ake kai wa Iran.
Wannan na zuwa ne yayin da Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami kan biranen Isra'ila a matsayin martanin kashe manyan kwamandojin yakinta.
Jami'an tsaro a Isra'ila sun tarwatsa masu zanga-zangar saboda dokar ta-ɓaci da kuma fargabar makaman da Iran ke harbawa zai iya fadawa kan su.
Asali: Legit.ng
