Bidiyon magidancin da ya gwangwaje matarsa da sabuwar mota a asibiti bayan ta haifa 'dansu na farko

Bidiyon magidancin da ya gwangwaje matarsa da sabuwar mota a asibiti bayan ta haifa 'dansu na farko

  • Wata mata da ta tafi asibitin Tantra cikin Accra don ta haihu ta riski wani babban abun mamaki bayan fitowarta
  • Mijinta ya bayyanar mata da dalleliyar sabuwar mota a matsayin kyauta, saboda haifa masa dansa na fari
  • Hakan ya dauki hankalin 'yan kallon da suka ziyarci asibitin saboda wasu dalilai daban, inda suka kashe kwarkwatar idanunsu

Wani mutumi da yayi matukar iya soyayya ya bai wa matarsa mamaki a asibitin Tantra dake birnin Accra, inda ya bata kyautar dalleliyar sabuwar mota, ba tare da jimawa da haifar masa dansa na farko ba.

A bidiyon da wata mai amfani da kafar sada zumuntar Instagram, fitacciyar 'yar kasar Ghana, Bridget Otoo, wanda abun ya faru a kan idon ta a asibitin ta kasa natsuwa a lokacin da lamarin ke faruwa.

Kara karanta wannan

Da ya bai wa mahaifinsa hantarsa, an yi aikin cike da nasara, sun yi hotuna cikin farinciki

Bidiyon magidancin da ya gwangwaje matarsa da sabuwar mota a asibiti bayan ta haifa 'dansu na farko
Bidiyon magidancin da ya gwangwaje matarsa da sabuwar mota a asibiti bayan ta haifa 'dansu na farko. Hoto daga @bridget_otoo
Asali: Instagram
"Wannan mutumin da yayi matukar iya soyayya ya gwangwaje matarsa da dalleliyar mota a matsayin godiya da haifa musu dan su na fari... Hakan ya matukar kayatarwa. Ina taya masoyan murna#TantraCommunityClinic,"

Haka zalika, a bidiyon da aka wallafa an ga matar cikin tsananin farin ciki ya lullubeta tana murmushi, yayin da tayi kokarin rungumar jinjirin, gami da tabbatar da abunda idanunta ke gane mata.

Jama'a sun yi martani

Masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani ba su yi kasa a guiwa ba wajen yin tsokaci bayan kallon bidiyon mai matukar birgewa. Ga wasu daga cikin tsokacin da akayi:

Serwaa Amihere ta ce: "Ubangiji yaushe ne."
@paulina_dedaa_opoku tayi tsokaci: "Kyautar nakuda. Hakan yayi kyau."
@Zenobia_amoah ta kara da: "Kai wannan abun da ban sha'awa yake."

Kara karanta wannan

Mace tagari: Hoton diyar Abacha tana nuna kauna ga Buni yayin da yake cikin damuwa

Magidanci ya yasar da matarsa da 'ya'yansa a Najeriya, ya koma Spain da takardunsu

A wani labari na daban, iyalin da a halin yanzu suke cikin tsananin rudani bayan halayyar ban mamakin da jigon iyalin yayi.

A da can iyalin suna rayuwa ne a Turai, amma a yanzu suna zaune a Najeriya, yayin da mijin ke zaune a kasar Spain. Chinedu ya dauki iyalinsa zuwa Najeriya kamar yadda ya saba zuwa gida hutu.

An samu labarin yadda mijin, wanda shi ne jigon iyalin, mai suna Chinedu, ya dauko iyalinsa daga kasar Spain da suke zaune da sunan hutu zuwa gida Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel