Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

  • Wasu mutanen da ke rayuwa tsakanin Kebbi da garin Zamfara sun wayi gari da labari mai dadi
  • Ana fama matsala da matsalar tsaro a jihohin Arewa maso yammacin Najeriya, musamman Zamfara
  • Wadanda ke zama a kusa da rafin ‘Yarkaka, sun ga gawawwakin wasu miyagu da sojoji suka kashe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kebbi - Mazauna yankin Kebbi da Zamfara sun samu gawar akalla mutane 23 da ake zargin cewa ‘yan bindiga ne da sojojin kasar nan suka hallaka.

Rahoton da HumAngle ta fitar ta bayyana cewa an tsinci gawar mutanen ne dauke da kayan sojoji a ranar 16 ga watan Yuni 2022 a gabar rafin Yarkuka.

Wannan rafi ne ya yi wa jihohin Zamfara da Kebbi iyaka a Arewa maso yammacin Najeriya.

Gawawwakin da aka tsinta cike su ke da raunuka a kai, fuska, kirji, wuya da kafafuwa. Ana kyautata zaton sojoji suka harbe wadannan mutane.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36

Yadda abin ya faru - Mai Aski

Wani Wanzami a kauyen Yarkuka mai suna Samuel ya shaidawa jaridar cewa sun iske gawawwaki su na yawo a kan ruwa bayan harbe-harbe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel mai shekara 37 a Duniya ya ce ya tabbata gawan na ‘yan ta’adda ne da suka gwabza da rundunar sojoji da ‘yan sanda masu aikin-kar-ta-kwana.

Sojojin Najeriya
Wasu Dakarun Sojojin Najeriya Hoto: www.aljazeera.com
Asali: UGC

Bugu da kari, Mai askin ya ce jami’an tsaron sa-kai sun yi kokari wajen ganin bayan ‘yan ta'addan. Wannan lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Yunin nan.

Abin farin ciki

Mazauna garin sun yi ta murna da suka ci karo da gawawwaki domin kuwa za su samu zaman lafiya tun da an hallaka mafi yawan miyagun da su ke ta’adi.

Shugaban ‘yan banga na Maga, Abubakar Kegudu ya ce da su aka yi ba-ta-kashin da ya yi sanadiyyar aika da-dama daga cikin ‘yan ta’addan barzahu.

Kara karanta wannan

Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra

An rasa mutane a Ukraine

Mun samu rahoto mutane 85 suka tashi daga Najeriya da zimmar taimakawa sojojin Ukraine a kan kasar Rasha a dalilin kudin da gwamnati ta ke yi biya.

A karshe kusan 45% na wadannan sojoji haya sun mutu, wasu daga cikinsu kuma sun dawo Najeriya. Rasha tce sojojin Najeriya 12 aka bari a filin daga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel