Da dumi-dumi: An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas

Da dumi-dumi: An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tsallake rijiya da baya, yayin da wasu tsageru suka farmaki tawagarsa a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni
  • Hakan ya faru ne yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC a jihar Legas
  • Majiyoyin yada labarai sun tattaro cewa Tinubu yana kan hanayar komawa gidansa ne bayan ya ziyarci Oba na Legas lokacin da aka farmake shi

A ranar Lahadi ne wasu ‘yan daba suka far ma motar bas din da ke dauke da ma’aikatan ofishin gwamnan jihar Legas a tsakanin Ebute-Ero da Adeniji, na yankin Iga-Iduganran a Legas, inda ‘yan jarida akalla biyu suka samu raunuka, wasu kuma suka kuje a jikinsu.

'Yan daba sun afkawa 'yan jaridan ne da ke cikin ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

An farmaki Tinubu a garinsa
Da dumi-dumi: An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas | Hoto: ait.live
Asali: UGC

An rahoto cewa, tsagerun sun kuma jefi motocin da ke cikin ayarin da ya kunshi jiga-jigan siyasa ciki har da Gwamna Babajide Sanwo-Olu; Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje; da sauran wadanda suka bar fadar Oba na Legas, Oba Rilwanu Akiolu.

Tinubu, wanda ya isa filin jirgin sama na Legas da misalin karfe 3:40 na rana, ga dandazon dimbin masoya da magoya bayan jam’iyyar, ya nufi fadar Oba Akiolu a ziyarar ban girma da ya kai masa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa, yayin da harin bai shafi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba, wasu da aka samu a motocin kusan biyu sun jikkata sakamakon harin.

Daga cikin wadanda suka jikkata har da 'yan jarida biyu da aka ce suna samun kulawar likitoci, inji rahoton This Day.

Poly Bauchi: Babbar ma'aikaciya ta rasa aikinta bisa shiga siyasa da tallata su Tinubu

Kara karanta wannan

Yan majalisa na shirin tsige mataimakin gwamna bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

A wani labarin, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Abubakar Tatari Ali a Bauchi, ta dakatar da wata babbar ma’aikaciya, Misis Raliya Kashim, bisa zargin hannu dumu-dumi a shiga siyasar da ya sabawa dokar aikin gwamnati.

Kakakin kwalejin, Malam Maimako Baraya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Bauchi, Punch ta ruwaito.

Baraya ya ce an dakatar da Raliya ne saboda yi wa wasu ‘yan takarar shugaban kasa da na gwamna kamfen ta shafinta na WhatsApp.

Asali: Legit.ng

Online view pixel