Tsohon Shugaban Najeriya ya samu sauki bayan ya kwanta jinya a asibitin kasar waje

Tsohon Shugaban Najeriya ya samu sauki bayan ya kwanta jinya a asibitin kasar waje

  • Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) ya fara samun sauki bayan ya shafe kwanaki yana gadon asibiti
  • Ana ta rade-radin zuciyar tsohon shugaban Najeriyar ta buga, amma ba haka gaskiyar abin yake ba
  • Abdulsalami Abubakar ya ga Likita a kasar waje ne domin a duba gwiwarsa da ta hana shi tafiya

United Kingdom - Tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) ya baro asibitin Landan inda aka kwantar da shi na wasu ‘yan kwanaki.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa dattijon ya bar asibiti bayan kammala jinyar rashin lafiya. Jaridar ta ce ba a san abin da ke damun tsohon shugaban ba.

A makon da ya gabata ne aka sheka da Abdulsalami Abubakar zuwa kasar Birtaniya domin ya ga Likita, a lokacin ne aka taya shi murnar cika shekara 80.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan jinya a Landan, an sallami tsohon shugaban Najeriya a asibiti

Wannan rashin lafiya ta sa Janar Abubakar mai ritaya ya dakatar duk ayyukan gabansa, har da sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a zaben jihar Ekiti.

Abdussalami ya samu bugun zuciya?

A ranar Litinin din da ta wuce rade-radi suka fara yawo cewa tsohon sojan ya samu bugun zuciya. Daga baya an fahimci cewa wannan labari ba gaskiya ba ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Garba Shehu wanda yake magana da yawun bakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya samu damar haduwa da Abdulsalami Abubakar a asibiti.

Abdussalami Abubakar
Tsofaffin Shugabannin Najeriya a taro Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Hadiman shugaban kasar ya tabbatar da cewa rashin lafiyar ba ta kai yadda ake zuzutawa ba.

An rahoto Shehu yana mai godiya ga Allah a kan yadda ya samu ganin dattijon, yake cewa hankalinsa ya karkata kan abubuwan da suke faruwa a gida.

The Cable ta rahoto tsohon shugaban sojan yana cewa ya baro asibiti, ya kuma ce gwiwarsa kurum aka duba saboda ya gagara yin tafiya a cikin watan Mayu.

Kara karanta wannan

Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

Likitoci sun ce a ketare

Janar din ya ce Likitocinsa sun bada shawarar ya tafi kasar waje domin a duba gwiwar, wannan ya sa ya soke duk bukukuwan taya shi murnar cika shekara 80.

“Gwiwa na ya kumbura, na yi kwana da kwanaki ba na iya tafiya a makon karshe na watan Mayu.”
“Bayan an duba, sai Likitocina suka bada shawarar in nemi kwararru a kasar waje su duba. Shiyasa na soke shirye-shiryen bikin zagayowar ranar haihuwa ta.”

- Abdulsalami Abubakar

Katin zabe na PVC

Ku na da labari Farfesa Mansur Sokoto ya ce duk wanda ba shi da katin zaɓe ya garzaya ya je ya yi, domin dole ne sai an zaɓi shugabanni da za su jagoranci al’umma.

Babban malamin Hadisin da tarihin addinin Musulunci yana cewa ba uzuri ba ne mutum ya ce ko an zabi shugabanni, manya za su tafka murɗiya domin abin na Allah ne.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel