Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

  • Bayan da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da wasu a coci, sun nemi a tara makudan miliyoyi domin sako jama'ar
  • Wannan na zuwa ne ta bakin shugaban yankin da 'yan bindigan suka sako, wanda yana daya daga cikin wadanda aka sace
  • Ya kuma bayyana yadda lamarin ya faru, inda ya ce sun yi tafiyar tazara mai tsawo kafin isar su mafakar 'yan ta'addan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Shugaban Angwan Fada da ke kauyen Rubu inda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu jama'ar coci a ranar Lahadi, Elisha Mari ya fita daga hannunsu kuma sun nemi ya tara Naira miliyan 100 domin a sako mutanensa.

Elisha Mari wanda yana daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, ya yi magana da manema labarai a ranar Litinin bayan da masu garkuwan suka sako shi, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

Ana neman kudin fansa N100m kan wasu mutane 30 na Kaduna
Musaya: 'Yan bindiga sun sako hakimi kan ya tara N100m ya karbi mutanensa 30 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Rahotanni a baya sun bayyana yadda ‘yan bindiga suka kai hari cocin Maranatha Baptist da cocin St Moses Catholic da ke Robuh, Ungwan Aku, karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna a ranar Lahadi; inda aka kashe mutanen yankin uku tare da sace sama da 30.

An ce ‘yan bindigan sun mamaye yankin ne a kan babura kusan 30, kowanne yana dauke da ‘yan bindiga biyu zuwa uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da manema labarai a lokacin da shugabannin hukumomin tsaro da tawagar gwamnatin jihar Kaduna suka ziyarci yankin a ranar Litinin, Elisha Mari ya ce ‘yan bindigan sun far wa kauyukansu inda suka rika harbe-harbe tare da sace mutanensa.

Yadda aka dafi da mutanen

Ya ce sun kwashe kusan awanni biyu ana tafiya a cikin dajin kafin su isa ga mafakar masu garkuwa da mutanen.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36

“An sake ni ne saboda ni ne shugaban gargajiyan yankin amma sun ce in tara akalla Naira miliyan 100 kudin fansa kafin a sako wadanda aka yi garkuwa da su.”

Wani mazaunin yankin, Bashir Usman, ya ce mutane uku da ‘yan bindigan suka kashe a harin na ranar Lahadi, lokacin da suka yi yunkurin kalubalantar ‘yan ta’addan.

Al’ummar yankin na cikin fargaba kuma har yanzu ba a koma daidai ba, duk da cewa jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a yankin da abin ya shafa da kewaye.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36

A wani labarin, akalla mutane 36 ne aka ruwaito an yi garkuwa da su a wani harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna ranar Lahadi.

Mazauna kauyukan ne suka bayyana hakan a wata ganawa da jami’an tsaro a ranar Litinin, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas

Mazauna yankin sun ce hare-haren da ake kai wa a kai a kai ya shafi rayuwarsu, domin ba za su iya zuwa gonakinsu ba a halin yanzu don gudun kada ‘yan bindiga su kashe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel