Latest
Majalisar wakilai ta nuna damuwa kan halin rashin tsaro da ake fama da shi a wasu yankunan jihar Borno. Ta bukaci gwamnatin tarayya ta tura karin jami'an tsaro.
Majalisar wakilan tarayya ta bukaci ministan sadarwada hukumar NCC su dakatar da shirin ƙarin kudin kira da sayen data, ta ce akwai bukatar inganta sabis.
Dauda Kahutu Rarara ya saki waka ta biyu, a jerin wakoki 9 na caccakar shugaban Nijar, Tchiani, yayin da Kosan Waka ya fitar da waka mai kare Tchiani.
Babban bankin Najeriya, CBN ya kawo sabon tsarin cajin kudi ta ATM. Za rika cire N100 kan kowane N20,000 idan mutum ya cire kudi ta ATM din da ba na bankinsa ba.
Bayan ware miliyoyi saboda daukar nauyin Musulmi zuwa aikin hajji, wasu 'yan asalin Ebonyi sun bukaci Majalisar Dokokin jihar Ebonyi ta tsige Gwamna Francis Nwifuru.
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi hadaka da masana daga Saudiyya domin habaka noman dabino, za a mayar da Jigawa mafi yawan noma da samar da dabino a Najeriya da Afrika.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci ministocin gwamnatinsa su fito su gaya wa ƴan Najeriya ayyukan da suka yi tun bayan naɗa su a muƙamin.
Hon. Amos Magaji ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC saboda rikicin cikin gida, inda Chinda ya bukaci a ayyana kujerarsa a matsayin babu kowa.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufa'i na shaida wa masu shirin cafke shi a gwamnatin Tinubu wurin da za su same shi nan da kwanaki kadan masu zuwa.
Masu zafi
Samu kari