"Ku Fito Ku Yi Bayani," Shugaba Tinubu Ya Hurowa Ministoci Wuta kan Ayyukan da Suke Yi

"Ku Fito Ku Yi Bayani," Shugaba Tinubu Ya Hurowa Ministoci Wuta kan Ayyukan da Suke Yi

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci ministocinsa su bayyana wa ƴan Najeriya ayyukan ci gaban da suka aiwatar tun baya naɗa su
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idirs ne ya sanar da umarnin Tinubu a wani taron manema labarai a Abuja yau Talata
  • Idris ya ce hakan zai ba ƴan Najeriya damar sanin ayyukan gwamnatin Bola Tinubu da kuma yin tambayoyi kan abubuwan da ba su gane ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya huro wa ministocin gwamnatinsa wuta kan ayyukan da suka yi tun bayan naɗa su a muƙamin.

Shugaban kasar ya umarci dukkan ministocin gwamnatinsa da su fito bainar jama'a su yi bayanin ayyukan da suka aiwatar tun daga lokacin da suka hau kujerar

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram 129,000 sun tuba, ana ba 800 horo na musamman

Shugaba Tinubu.
Bola Tinubu ya umarci ministoci su gaya wa ƴan Najeriya ayyukan ci gaban da suke yi a ƙaar nan Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubi
Asali: Twitter

Vanguard ta ce ministan watsa labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana umarnin na shugaban kasa a wani taron manema labarai a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Tinubu na ɗaukar wannan matakin

A cewar ministan, wannan mataki na bayar da bayanai zai bai wa ‘yan Najeriya damar sanin irin ayyukan da gwamnati ta aiwatar tun daga zuwanta kan mulki.

Mohammed Idris ya ce idan ƴan Najeriya suka san ayyuka kowane minista za su samu damar yin tambayoyi kan abubuwan da suka shafi mulkin kasar nan.

Ministan ya ce wannan yunkuri na gwamnatin Tinubu na nufin kara inganta hulɗa da jama'a da bayyana ci gaban da ake samu a bangarori daban-daban.

Gwamnatin Tinubu ta shriya taron ministoci

Mohammed Idris, ya bayyana shirin fara taron ministoci na lokaci-lokaci a mako mai zuwa gabanin cika shekara biyu da kafa gwamnatin shugaba Bola Tinubu. 

Ya ce a wannan karon, taron ministocin zai maida hankali ne kan ayyukan da gwamnati ta aiwatar daga shigowar shekarar 2025 zuwa yau, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

"Shugaba Tinubu ya himmatu wajen tabbatar da cewa gwamnatinsa na yin komai a buɗe, kuma wannan taron ministocin na ɗaya daga matakan cimma wannan buri," in ji Mohammed.

Gwamnatin Tinubu ta fara karɓar harajin motoci

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta fara aikin karbar haraji a kan babban titin Abuja–Akwanga–Lafia–Makurdi.

Rahoto ya nuna cewa direbobin da ke bin wannan hanya za su fara biyan haraji wanda ya fara daga daga N500 ga kananan motoci har zuwa N1,600 ga manyan motoci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262