An Bukaci Tsige Kiristan Gwamna da Ya Ware N551m domin Daukar Nauyin Hajjin Musulmi

An Bukaci Tsige Kiristan Gwamna da Ya Ware N551m domin Daukar Nauyin Hajjin Musulmi

  • Wasu 'yan asalin Ebonyi da ke ƙetare sun bukaci Majalisa ta tsige Gwamnan jihar saboda amincewa da N551m don daukar nauyin aikin Hajji
  • Kungiyar AEISCID ta soki matakin gwamnan, tana mai cewa hakan ya saba doka, kuma ya kamata a mayar da hankali kan rage talauci a jihar
  • Shugaban kungiyar, Paschal Oluchukwu ya ce kashe miliyoyin naira kan aikin Hajji ba tare da amincewar majalisa ba ya saba kundin tsarin mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Abakaliki, Ebonyi - An taso Gwamna Francis Nwifuru a gaba kan ware miliyoyi saboda daukar nauyin Musulmi zuwa Hajji a Ebonyi.

Matakin gwamnan ya fuskanci suka daga ɓangarorin jihar saboda amincewa da N551m don aikin Hajji na 2025.

An nemi majalisa ta tsige Gwamna kan ware miliyoyi saboda aikin hajji
Kungiya ta bukaci tsige Gwamna Francis Nwifuru kan ware N551m saboda aikin hajji. Hoto: Rt. Hon. Francis Nwifuru.
Asali: Facebook

Hajji: Kungiya ta gargadi Gwamna Nwifuru

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Legit ta samu wanda shugabanta, Paschal Oluchukwu ya fitar a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe ta fusata, an ba da umarnin farauto makasan malamin addini

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata kungiya mai suna Association of Ebonyi Indigenes Socio-Cultural in the Diaspora (AEISCID) ta bukaci Majalisa ta tsige shi idan har ya ci gaba da shirin daukar nauyin musulmai 46 zuwa Hajji.

Kungiyar ta bukaci Gwamna Nwifuru ya janye wannan shiri, tana mai cewa bai kamata kudaden haraji su tafi ga aikin Hajji ba.

Shugaban kungiyar ya ce kashe N551m kan aikin Hajji yayin da jama’a ke fama da talauci babban rashin adalci ne.

"Majalisar Dokokin Jihar Ebonyi ta gaggauta fara tsige gwamna idan ya ci gaba da wannan shiri don tallafawa kowane addini."
"Babu tanadi irin wannan na kashe kudi a kasafin kudin 2025, matakin gwamnan ya sabawa Sashe na 120 (3 & 4) na Kundin Tsarin Mulki na 1999.
"Dokar kasa ta bayyana cewa ba a iya fitar da kudi daga asusun jihar ba tare da izinin dokar majalisa ba."

Kara karanta wannan

'Gwamnati ta kawo sabon haraji da zai jawo tashin farashi,' Saraki ya tono magana

- Paschal Oluchukwu

Kungiya ta fadi fannonin da ya kamata a kula

AEISCID ta bukaci gwamnatin jihar ta mayar da hankali kan rage talauci a Ebonyi, maimakon kashe kudi a aikin Hajji.

A ranar da gwamnati ta amince da N551m don aikin Hajji, ita ce rana guda da ta ware N300m kacal don bunkasa rayuwar mutane 300 a jihar.

Wannan yasa kungiyoyin farar hula ke sukar gwamnan, suna mai cewa ba daidai ba ne a fifita Hajji fiye da inganta rayuwar al’umma.

Gwamna Nwifuru ya ware N551m saboda aikin hajji

A wani labarin, Gwamnatin jihar Ebonyi ta bukaci shugabannin kananan hukumomi 13 su dauki nauyin akalla Mahajjaci daya don aikin Hajjin 2025.

Majalisar zartarwa ta jihar ta amince da kashe N551m domin daukar nauyin Mahajjata 46, yayin da kowane shugaban karamar hukuma zai dauki guda daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.