Masanan Saudiyya Sun Shigo Najeriya domin Bunkasa Noman Dabino a Jigawa

Masanan Saudiyya Sun Shigo Najeriya domin Bunkasa Noman Dabino a Jigawa

  • Gwamnatin Jihar Jigawa ta kulla yarjejeniya ta musamman da kamfanonin Saudiyya da Najeriya domin haɓaka noman dabino a jihar
  • Masana daga Saudiyya za su kawo sababbin fasahohi da dabarun noma don samar da ingantaccen dabino domin habaka nomarsa
  • Mai girma Gwamna Umar Namadi ya ce shirin zai ƙara wa jiharJigawa ƙarfin noma da fitar da dabino zuwa kasuwannin duniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - A kokarin bunƙasa tattalin arziki ta bangaren noma, Gwamnatin Jigawa ta kulla haɗin gwiwa da masana daga Saudiyya domin haɓaka noman dabino a jihar.

Gwamna Umar Namadi ne ya karɓi wata tawaga daga Saudiyya wacce ta ƙunshi ƙwararru kan noman dabino, karkashin jagorancin Abdul’aziz Abdurrahman Al-Awf.

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

Noman dabino
Jigawa ta yi hadaka da Saudiyya kan noman dabino. Hoto: Garba Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da kakakin gwamnan, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar ta bayyana shirin haɗin gwiwa da Jigawa domin amfani da sababbin fasahohi da dabarun noma don ƙara yawan da ingancin dabino da ake nomawa a jihar.

Za a bunkasa noman dabino a jihar Jigawa

Shugaban tawagar Saudiyya, Abdul’aziz Al-Awf, ya bayyana cewa suna da niyyar shigo da sababbin dabarun noma don tabbatar da cewa ana samun dabino a ko da yaushe.

Abdul’aziz Al-Awf ya ce za a rika samar da dabino a cikin shekara baki ɗaya, maimakon lokaci-lokaci kamar yadda ake yi a yanzu.

Ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwar da za su yi da Jigawa zai haɗa da horar da manoma, ba wa matasa damar yin sana’a, da shigo da shahararrun nau’ikan dabino daga Saudiyya.

“Ba kawai za mu ƙara yawan dabinon da ake nomawa a Jigawa ba, har ma za mu inganta ingancinsa domin Jigawa ta zama cibiyar noman dabino a Najeriya da ma Afrika,”

Kara karanta wannan

"Najeriya ta yi Rashi," Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa fitaccen malamin Musulunci rasuwa

- Abdul’aziz Al-Awf

Noman Dabino: Bayanin gwamnan Jigawa

Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cikakken goyon bayan gwamnatinsa ga shirin, yana mai cewa yana daidai da manufofin jihar na haɓaka noma.

“Muna maraba da ku a Jigawa kuma muna matuƙar godiya da sha’awarku na yin aiki tare da mu.
"Haɗin gwiwar za ta kawo ci gaba ga al’ummarmu, kuma muna da himmar ganin an kafa gonakin dabino a duk faɗin jihar,”

- Umar Namadi

Ya kuma bayyana cewa Jigawa ita ce jagaba wajen noman alkama a Najeriya, kuma yana da burin ganin jihar ta zarce buƙatun cikin gida har ta fara fitar da dabino zuwa ƙasashen waje.

Maganar fitar da dabino kasashen ketare

Gwamna Namadi ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta samar da dukkanin kayan aiki da goyon bayan da ake bukata don ganin shirin ya cimma nasara.

Kara karanta wannan

'Gwamnati ta kawo sabon haraji da zai jawo tashin farashi,' Saraki ya tono magana

“Muna fatan ganin Jigawa ta zama cibiyar noman dabino na kasuwanci, ba kawai don amfanin cikin gida ba, har ma don fitarwa zuwa kasashen waje.
"Tare da fasahohi da ilimin da za ku shigo da su, za mu sauya fasalin noma a jihar, mu samar da ayyukan yi, mu kuma bunkasa tattalin arzikin al’ummarmu,”

Tawagar Saudiyya tare da kamfanin Netay Agro-Tech sun ziyarci wasu yankunan da ake noman dabino a Jigawa domin tantance ƙasa da yanayin da ya dace da noma.

Shugaban kamfanin Netay Agro-Tech, Abubakar Musa Bamai, ya bayyana cewa sun riga sun gudanar da bincike kan ƙasa tare da masana harkar noma.

Za a raba tallafi ga manoma a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta fitar da shirin tallafawa manoma da yawansu ya kai 30,000.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin za ta raba tallafin Naira biliyan 3.5 ga manoma domin habaka tattali da samar da abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng