Jam'iyyar APC Ta Jijjiga PDP a Kaduna, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheka
- Hon. Amos Magaji, dan majalisar wakilai mai wakiltar Zangon Kataf/Jaba, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC saboda rikicin cikin gida
- Magaji ya bayyana cewa rikice-rikicen PDP a matakin ƙasa da mazabu sun sa ya ga ba zai iya ci gaba da zama a cikin jam'iyyar ba
- Shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ya musanta zargin rikici a PDP tare da bukatar a ayyana kujerar Magaji a matsayin babu kowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Dan majalisa mai wakiltar Zangon Kataf/Jaba a majalisar wakilai, Amos Magaji, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta wasikar Magaji na sanar da sauya shekar a zaman majalisar na ranar Talata.

Asali: Twitter
'Dan majalisar PDP ya koma jam'iyyar APC
A cewar Magaji, rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a matakin ƙasa da mazabu ya tilasta masa ficewa daga jam’iyyar, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa duk kokarin warware matsalolin bai haifar da ɗa mai ido ba, don haka ya ga ya dace ya sauya sheka.
Yayin da dan majalisar ya ce akwai rigingimu a PDP, a hannu daya, Hon. Kingsley Chinda, shugaban marasa rinjaye, ya musanta batun rikici a jam'iyyar.
An nemi a wofantar da kujerar Hon. Amos
Hon. Chinda ya bukaci Abbas ya ayyana kujerar Magaji a matsayin babu kowa a kanta bisa tanadin sashe na 68 na kundin tsarin mulkin 1999.
Amma Abbas ya mayar da martani yana mai bukayar Chinda ya rubuta masa takarda a hukumance idan yana son wannan buƙatar.
A ‘yan makonnin da suka gabata, wasu ‘yan majalisa daga PDP da Labour Party sun koma APC, inji rahoton The Cable.
A ranar 2 ga Oktoba, Chris Nkwonta, mai wakiltar Ukwa gabas/Ukwa yamma a jihar Abia, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan
'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023
Haka zalika, a ranar 30 ga Oktoba, Sulaiman Abubakar mai wakiltar Gummi/Bukkuyum a jihar Zamfara, ya koma APC daga PDP.
'Yan majalisar LP sun taru, sun koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu ‘yan majalisar wakilai hudu na jam'iyyar LP sun sauya sheka zuwa APC a yayin zaman majalisar tarayyar.
Ɗan majalisar wakilai, Benedict Etanabene, ya soki matakin da ƴan jam'iyyarsa ta LP suka ɗauka na komawa APC, yana mai cewa sun yi haka ne don zaben 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng