Tsohon Gwamna El Rufa'i Ya Yi Maganar Shirin Gwamnatin Tinubu na 'Cafke' Shi
- Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya na sane da rade-radin cewa ana son sa jami'an gwamnati su kama shi
- Wannan na zuwa ne a matsayin amsa ga wani sako da ke ankarar da tsohon gwamnan cewa an shirya manakisar yadda za a damke shi
- Ya kara da cewa kama wa, tsare wa da azabtar da 'yan hamayya ba sabon abu ba ne a siyasa, saboda haka wannan ba zai firgita shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa bai damu da jita-jitar shirin cafke shi ba saboda sukar da yake yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce barazanar kama shi ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya, tare da jaddada cewa wannan ba za isa ya tsorata ya gudu daga kasarsa ba.

Asali: Facebook
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, El-Rufai ya ce tun a watan Yuli 2024, lokacin da rahoton Majalisar Jihar Kaduna ya fara yawo, ake ta yayata cewa gwamnati za ta sa a damke shi."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan martani ne ga wani Imran U Wakili, masoyinsa da ya bayyana fargabar jami'an gwamnati na shirin kama tsohon gwamnan a shafin X.
"Ba zan yi gudun hijira ba" — Nasir El-Rufai
Tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya ce an yi ƙoƙarin tsoratar da shi ta hanyoyi daban-daban, ciki har da aika masa saƙonnin barazana ta hanyar abokansa da makusantansa.
Ya ce:
“Sun aika irin waɗannan saƙonnin tsoratarwa da barazana ga abokaina, iyalaina da abokan siyasa na da nufin su sa ni in bar ƙasa da kai na. Amma ba zan tafi ba.”
“Na dakatar da duk wasu shirye-shiryen karatun da nake da su, har da koyon sababbin harsuna, kuma zan fi kasancewa a Najeriya fiye da yadda na ke a baya.”

Kara karanta wannan
'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023
El Rufa’i: "Na daina yin shiru"
El-Rufai ya jaddada cewa ba zai yi shiru ba, yana mai cewa zaluntar ‘yan adawa abu ne da aka saba da shi a tarihin siyasa.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa:
“An taɓa kama ni da tsare ni har sau uku a baya saboda bayyana ra’ayina kan gwamnatoci da suka gabata.
El-Rufai ya fadi inda za a same shi
Tsohon gwamnan Kaduna ya tura sako na kai tsaye zuwa ga masu shirin damke shi, inda ya tabbatar da cewa zai shigo Najeriya domin halartar wani babban taro da za a yi a nan kusa.
Ya ce:
“Su sani cewa zan dawo domin halartar ƙaddamar da littafin tarihin tsohon Shugaban kasa, IBB, in sha Allah, a ranar 20 ga watan Fabrairu.”
“Da Allah mu ka dogara,” Inji El Rufa’i
Nasir El Rufa’i ya bayyana cewa da Allah SWT kadai ya dogara, saboda haka duk wata barazana da za a yi masa, ba za ta say a ji dar a cikin ransa ba.

Kara karanta wannan
Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji
Ya jaddada imaninsa da cewa:
“Muna dogara ga Allah kaɗai. Ba ma tsoron wani mutum face Allah Madaukakin Sarki. Muna fatan alheri, amma muna shirin fuskantar duk wani abu da ka iya faruwa.”
El Rufa'i ya fadi dalilan tallata Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya karyata zargin da ake masa na rashin goyon baya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a kakar zaɓen 2023.
A cikin sakon da ya wallafa, El-Rufai ya bayyana cewa ya yi duk abin da ya yi don Allah, jam'iyyarsa da ƙasarsa, ba tare da wata tsammani ta riba ba, kuma yanzu magana ta riga ta wuce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng