CBN Ya Kawo Sabon Tsarin Cire wa 'Yan Najeriya Kudi wajen Aiki da ATM

CBN Ya Kawo Sabon Tsarin Cire wa 'Yan Najeriya Kudi wajen Aiki da ATM

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke damar cire kuɗi kyauta da ake yi da katin ATM sau uku a wata a bankunan da mutum ba shi da asusu
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa cewa sabuwar dokar za ta fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2025, kamar yadda sanarwar CBN ta bayyana
  • Za a fara karbar N100 kan duk N20,000 da aka cire a ATM na wani banki, kuma za a iya ƙarin har N500 idan injin a wajen harabar banki yake

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da sauya tsarin cajin kudi ta hanyar ATM a fadin ƙasar nan, wanda ya haɗa da soke damar cire kuɗi kyauta sau uku a wata.

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

Sanarwar ta fito ne daga wata takarda da Mukaddashin Daraktan Tsare-tsare da Kula da Harkokin Kuɗi na CBN, John Onojah, ya sanya wa hannu ranar Talata.

CBN ATM
CBN ya kawo sabon caji wajen cire kudi ta ATM. Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Getty Images

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa sabuwar dokar za ta fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CBN ya bayyana cewa matakin na da nufin inganta tsarin ATM, rage hauhawar farashi, da kuma ƙarfafa saka hannun jari a fannin.

Sabon harajin cire kudi ta ATM a Najeriya

Sabuwar dokar CBN ta yi watsi da tsohuwar damar da ke bai wa kwastomomi damar cire kuɗi kyauta sau uku a wata daga ATM a bankunan da ba su da asusu.

Sanarwar ta nuna cewa daga yanzu, duk wanda ya cire kuɗi a ATM na wani banki zai fuskanci caji kai tsaye ba tare da wata dama ta cire kudi kyauta ba.

Punch ta wallafa cewa CBN ya ce sabon cajin yana da matuƙar muhimmanci don tabbatar da cewa an inganta tsarin ATM a Najeriya.

Kara karanta wannan

Harsashi ya kare wa dan bindiga yana musayar wuta da sojojin Najeriya

Ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa saka kuɗi don ƙara yawan na’urorin ATM a fadin ƙasar.

Sabon cajin da za fara ta ATM

Sabuwar dokar da za a fara aiki da ita daga ranar 1 ga Maris, 2025, ta tanadi:

Cire kudi a bankin da mutum ke da asusu

  • Idan kwastoma ya cire kuɗi daga ATM na bankinsa, ba zai biya ko sisin kwabo ba

Cire kudi a bankin da mutum ba shi da asusu

  • Za a caji N100 kan kowane N20,000 da aka cire kudi ta ATM da ke cikin harabar banki
  • Za a caji N100 kan kowane N20,000 da aka cire, tare da ƙarin N500 idan aka cire kudi ba a harabar banki ba
  • Idan aka yi mu'amalar kudi daga kasashen waje, za a caji kwastoma bisa ga adadin da kamfanin da ke sarrafa ATM ɗin ƙasashen waje ya sanya.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An maka Shugaba Tinubu a kotu kan badakalar kwangilar Naira biliyan 167

Dalilan CBN na sabunta tsarin cajin ATM

Babban Bankin Najeriya ya ce babban dalilin sauyin shi ne ƙara yawan ATM a faɗin ƙasar da kuma tabbatar da cewa kwastomomi suna biyan kuɗin aiki da bankuna suka musu.

A cewar CBN, tsarin tsohon caji na cire kuɗi kyauta yana hana bankuna saka kuɗi a injunan ATM, wanda ke hana ƙaruwa da yawan ATM a Najeriya.

CBN ya saka tara ga bankuna

A wani rahoton, kun ji cewa bankin CBN ya yi hukunci mai tsauri kan wasu bankunan da ba su samar da wadataccen kudi.

Banckin CBN ya ware wasu bankuna ya sanya musu tarar sama da Naira biliyan 1 a matsin horo kan rashin samar da takardun kudi ta ATM.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng