Latest
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa 'yan kasar nan da ke magana kan Natasha ba su da masaniya a kan al'amuran majalisa.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya sauya sheka daga APC zuwa SDP. Wasu na hannun damansa sun ce dama akwai alamar hakan kuma ba sa mamaki.
Rahotanni na nuni da cewa Nasir El-Rufai ya bar APC kuma zai shiga SDP, yayin da majiyoyi da dama ke tabbatar da wannan matakin. Dansa Bashir ya ba da alama.
Jam'iyyar adawa a jihar Ribas watau APC ta ba Gwamna Siminalayi Fubara awanki 48 ya yi murabus daga muƙaminsa ko kuma Majalisar dokoki ta tsige shi.
Sheikh Dr. Jabir Sani Maihula ya ba da fatawa kan fitar maziyyi, goge baki da man gogewa da wasu abubuwa da ake tunanin suna karya azumi amma ba haka bane.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Chief Patrick Adaba, ya rasu yana da shekaru 79 a ranar Lahadi a Abuja, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Gwamnatin Bola Tinubu ta amince da samar da motoci masu aiki da wutar lantarki 10,000 a wasu Arewa maso Gabas. Za a samar da wuraren cajin motocin.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana cewa ta kwato kudade mafi yawa a shekarar 2024 daga hannun barayin da suka sace kudin gwamnati.
Wasu daga cikin manyan mata 'yan siyasa a Najeriya da aka yi zaton za su mara wa Natasha Akpoti Uduaghan baya sun nuna ba su tare da ita kan dambarwarta da majalisa.
Masu zafi
Samu kari