Latest
Coronavirus na ci gaba da yaduwa a Najeriya duk da gwamnatin Najeriya na ci gaba da kokarin shawo kan annobar. A yanzu jimillar masu cutar ya kai 7,389 a kasar.
Mutum 1 ya mutu, wasu da dama sun jikkata a wasy hadarurruka guda biyu da suka faru daban daban a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar 24 ga watan Mayu.
Kwakwalwa, ita ce gaba muhimmanci a jikin dan Adam, amma mutane da dama suna wasa da ita, basu san muhimmancin kulawa da ita bar, har sai mai aukuwa ta auku.
A halin yanzu dai akwai fiye da mutum miliyan biyar da annobar bakuwar cutar nan ta coronavirus ta harba cikin nahiyoyi da kasashe dari da 88 a fadin duniya.
A jiya ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya saki fursunoni 293 da ke zaman cin sarka a wani mataki na gyara hali cikin gidajen kaso da ke jihar.
Ministan kwadago Chris Ngige ya ce yana da damar fitowa takarar kowacce kujerar siyasa a 2023 har da ta shugaban kasa da na gwamnan jihar Anambra idan ya so.
Musulmai a wasu jihohi da ke Arewacin Najeriya, sun yi wa umarnin Sarkin Musulmi kunnen uwar shegu da yayin da suka yi taron jama'a wajen gudanar da sallar idi.
An sallami tsohon manajan daraktan hukumar TCN, Usman Gur ne a kan wata badakar wutar lantarki wacce ta kai kimanin dala biliyan biyu, kusan naira biliyan 781.
Buhari ya umarci sabon shugaban ma'aikatan fadarsa, Farfesa Ibrahim Agboola Gambari, ya soke nade-nade da kuma wasu ayyuka da marigayi Abba Kyari ya amince dasu
Masu zafi
Samu kari