Sallar Idi: Kano, Katsina da Borno sun yi wa Sarkin Musulmi kunnen uwar shegu

Sallar Idi: Kano, Katsina da Borno sun yi wa Sarkin Musulmi kunnen uwar shegu

A ranar Lahadi, musulmai a wasu jihohi da ke Arewacin Najeriya, sun yi wa umarnin Sarkin Musulmi kunnen uwar shegu inda suka yi taron jama'a yayin gudanar da sallar idi a bana.

Jihohin Kano, Katsina, Borno, Zamfara da kuma Bauchi, sun yi taron dumbin jama'a yayin gudanar da sallar idi da ta wakana a ranar Lahadi, 24 ga wata Mayun 2020.

Wannan lamari ya sabawa umarnin fadar Sarkin Musulmi da kuma kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin yaki da cutar korona a Najeriya (PTF), na cewa a guji taron jama'a yayin gudanar da sallar idin bana.

Binciken manema labarai na jaridar The Punch ya gano cewa, jama'a sun yi wa filayen sallar idi tsinke a jihohin na Arewa wanda hakan ya ci karo da matakan dakile yaduwar cutar korona da aka shar'anta.

Yana daga cikin sharudan da mahukuntan lafiya na duniya suka gindaya domin dakile yaduwar cutar korona, shi ne ba da tazara yayin shiga jama'a da kuma sanya takunkumin rufe fuska.

A makon da ya gabata ne jihohin Kano, Katsina, Borno da kuma Yobe, suka sassauta dokar kulle wadda gwamnatin tarayya ta shimfida, inda suka ba da damar a ci gaba da gudanar da ibada a wuraren ibadu.

Gwamnonin jihohin sun bai wa al'ummominsu damar ci gaba da gudanar da Sallar Juma'a sabanin yadda ta kasance a baya, da kuma ba da damar yin Sallar Idi yayin da aka kammala Azumin watan Ramadana.

Yadda shugabannin Kano suka gudanar da Sallar Idi a filin masallacin Idi da ke Kofar Mata
Yadda shugabannin Kano suka gudanar da Sallar Idi a filin masallacin Idi da ke Kofar Mata
Asali: Twitter

Sai dai majalisar Majalisar koli mai zartarwa a kan sha'anin addinin Islama bisa jagorancin Sultan na Sakkawato, Mai Martaba Alhaji Sa'ad Abubakar, a ranar Laraba ta fidda sabon umarni wanda ya ci karo da na gwamnatocin jihohin.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada Farfesa Obioma a matsayin sabon shugaban Hukumar NECO

Cikin sanarwar da babban sakataren majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya fitar ta bayyana cewa, "al'ummar Musulmi su guji yin taron jama'a a filin idi cikin manyen birane yayin gudanar da sallar idin bana."

Sai dai sanarwar ta ce "a iya gudanar da sallar a cikin masallatai inda za a iya takaita tururuwar jama'a domin lura da yadda za a kiyaye matakan ba da tazara wajen dakile yaduwar cutar korona."

Cikin wani sabon hukunci da kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) wadda ita ma Sarkin Musulmi ke jagoranta, ta sake fitarwa a ranar Alhamis, ta nemi musulmi da su gudanar da sallolin idin bana a cikin gida tare da iyalansu.

Hukuncin da ya fito daga bakin babban sakataren JNI, Dr Khalid Abubakar, ya ce "an dakatar da taron sallar idin bana, kuma ana umartar dukkanin musulmi a Najeriya da su gudanar da sallar idin a cikin gida tare da iyalansu."

Haka kuma yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, shugaban kwamitin yaki da cutar korona a Najeriya kuma sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, ya ba da shawarar a kauracewa taron jama'a yayin murnar bikin sallah a bana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel