An rasa rayuka biyu sakamakon gobara a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

An rasa rayuka biyu sakamakon gobara a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

A kalla gidaje 1,613 ne suka kone a garejin Muna inda ya kasance sansanin 'yan gudun hijira da ke Maiduguri.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya wallafa, mutum biyu ne suka samu miyagun kuna sakamakon gobarar.

Shugaban cibiyar taimakaon gaggawa ta jihar Yobe, Yabawa Kolo ya ce lamarin ya faru da yammacin ranar Idi ne.

Gwamnan Babagana Zulum ya ziyarci sansanin don tabbatar da yanayin barnar da gobarar tayi.

Zulum ya bayyana cewa, yawan gobarar da ake samu a sansanin na nuna bukatar rufe sansanin 'yan gudun hijira da ke fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta aminta da gina rukukunin gidaje dubu goma a fadin jihar don tallafawa 'yan gudun hijirar.

Ya ce za a fara ginin da gaggawa bayan an saki kudin don kawo karshen rayuwar da suke yi a sansanin gudun hijira.

A wata ukun farko na wannan shekarar, sansanin 'yan gudun hijira da ke Nganzai, Ngala, Mafa da Mungonu duk sun yi gobara sakamakon cunkoso da yawan mutane.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Wike ya saki N450m na diyyar mamatan zaben 2019

A wani lamarin kuma mun ji cewa mutum daya ya mutu, wasu da dama sun jikkata a wasy hadarurruka guda biyu da suka faru daban daban a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu.

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito shugaban hukumar kare haddura ta kasa na jahar Ogun, Clemet Oladele ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a garin Ogun a ranar Litinin.

Oladele yace hadarin farko ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a yankin Isaara kusa da Ogere a kan titin Ibadan zuwa Legas da ya rutsa da wata motar Bus kirar Toyota mai lamba AG 346XV.

Hadarin ya kunshi maza biyu a mace daya, inda motar ta kufce madirebanta sakamakon halin maye da yake ciki, wanda yasa ya yi ta gudun wuce sa’a a kan titin har ta kufce masa.

Daga karshe Oladele ya gargadi direbobi su kula da dokokin hanya da dokokin tuki musamman yayin da aka fara bude hanyoyi sakamakon sassauta dokokin zaman gida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel