Daya bayan daya: Yawan masu cutar korona a jihohi 35 na Najeriya

Daya bayan daya: Yawan masu cutar korona a jihohi 35 na Najeriya

- Cutar korona na ci gaba da hauhawa a Najeriya duk da kokarin gwamnatin tarayya na kokarin shawo kan ta

- Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta tabbatar da cewa an samu karin mutum 313 da suka sake kamuwa da cutar korona a ranar Lahadi

- Jimillar masu cutar a Najeriya a halin yanzu sun kai 7,389 a fadin jihohi 35 na kasar nan

Cutar Coronavirus na ci gaba da yaduwa a Najeriya duk da gwamnatin Najeriya na ci gaba da kokarin shawo kan annobar.

Hukumar kula da cutuka masu yaduwa (NCDC) a ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu, ta tabbatar da cewa an samu karin mutum 313 da suka kamu da cutar. A halin yanzu, jimillar masu cutar sun kai 7,389 a Najeriya.

Yanzu haka, jihohi 35 ne akwai masu cutar a kasar nan. Jihar Legas ce ke da mafi yawan masu cutar.

Ga jihohi da kuma yawan masu cutar a Najeriya:

1. Legas na da mutum 3,505.

2. Jihar Kano na da mutum 896.

3. Abuja tana da mutum 505.

4. Jihar Katsina ma da mutum 308.

5. Jihar Borno na da mutum 250.

6. Jigawa tana da mutum 241.

7. Jihar Oyo tana da mutum 240.

8. Bauchi tana da mutum 232.

9. Jihar Ogun na da mutum 231.

10. Jihad Edo na da mutum 191.

11. Jihar Kaduna na da 189.

12. Gombe na da mutum 145.

13. Jihar Rivers na da mutum116.

14. Sokoto tana da mutum 116.

15. Jihar Filato na da mutum 83.

16. Jihar Kwaea na da mutum 79.

17. Jihar Zamfara na da mutum 79.

18. Jihar Yobe na mutum 47.

19. Jihar Nasarawa na da mutum 46.

20. Osun tana da mutum 42.

21. Delta ma da mutum 39.

22. Jihar Ebonyi tana da mutum 33.

23. Jihar Kebbi na da mutum 32.

24. Jihar Neja na da mutum 28.

25. Adamawa na da mutum 27.

26. Akwa Ibom na da mutum 24.

27. Ondo na da mutum 23.

28. Jihar Ekiti na da mutum 20.

29. Jihar Enugu na da mutum 18.

30. Taraba na da mutum 18.

31. Bayelsa na da mutum 11.

32. Jihar Anambra na da mutum 9.

33. Imo na da mutum 7.

34. Jihar Abia na da mutum 7.

35. Sai jihar Binuwai da ke da mutum 5.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya soke nade-naden da marigayi Abba Kyari yayi

A yayin da jihar Legas ke kokarin ci gaba da harkokin kasuwanci, gwamnatin jihar na kokarin assasa amfani da takunkumin fuska a kananan hukumomi 57 na jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel