Arzikin Najeriya ya ja baya da kashi 1.87% saboda annobar korona - NBS
A wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar a kan yawan arzikin kasar wato GDP, ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya ja baya a rubu'in farko na bana.
Alkaluman da NBS ta fitar sun nuna cewa, yawan arzikin Najeriya ya yi mummunar faduwa da kashi 1.87 cikin dari a rubu'in farko na shekarar 2020.
Cikin rahoton da Hukumar ta fitar a ranar Litinin, ya nuna somin tabi a kan durkushewar da tattalin arzikin kasar zai yi sanadiyar annobar cutar korona.
Hakika an ja baya a arzikin kasar sanadiyar annobar da cutar korona ta haifar, wadda ta janyo faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya.
A yayin da Najeriya ta dogaro da arzikin man fetur da ma'adansa wajen samun kashi 90% na kudin shiga, dole ne a yanzu tattalin arzikin kasar ya ja baya saboda yadda kasuwar bukatarsa ta bushe.
A ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa ta Najeriya, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa kasar nan za ta sake shiga cikin wani sabon koma-bayan tattalin arziki.
Duba da yadda al'amuran kasuwanci suka tsaya cik a fadin duniya saboda annobar korona, Ministar ta ce babu makawa matsi ya tunkaro tattalin arzikin Najeriya.
Furucin Mrs. Ahmed ya zo ne yaynin ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar tattalin arzikin da ya gudana wanda mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
KARANTA KUMA: Jerin kasashe 12 da ba a samu bulla cutar korona ba a duniya
Ta ce tattalin arzikin Najeriya zai ja baya inda zai samu nakasu na kimanin kashi 4.4 cikin dari muddin likafar annobar ta ci gaba.
Sai dai ta ce idan har su ka dage wajen fadi-tashin daukan matakai da za su zamo tamkar ginshiki ga tattalin arzikin kasar, to kuwa nakasun da zai fuskanta bai wuce na kashi 0.4 cikin dari ba.
A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce karyewar da farashin danyen mai ya yi a kasuwar duniya alheri ne ga kasar Najeriya a fakaice.
Atiku ya ce kamata ya yi Najeriya ta ribaci halin da kasuwar man fetur ta shiga ciki, a matsayin wata dama ta yaye kanta daga dogaro a kan albarkatun man fetur wajen samun kudaden shiga.
Wazirin na Adamawa ya ce kamata ya yi faduwar farashin danyen mai a duniya ya kasance wani abun alfahari ga gwamnatin Najeriya da a yanzu za ta yiwa kanta karatun ta nutsu.
Atiku wanda ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019, ya gargadi Najeriya da ta tashi ta farga wajen sauya tunaninta na dogaro da man fetur.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng