Mutum 1 ya mutu, da dama sun samu munanan rauni a hadarurrukan mota
Mutum daya ya mutu, wasu da dama sun jikkata a wasy hadarurruka guda biyu da suka faru daban daban a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu.
Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito shugaban hukumar kare haddura ta kasa na jahar Ogun, Clemet Oladele ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a garin Ogun a ranar Litinin.
KU KARANTA: Bikin Sallah a Kaduna: Na yi wankan sallah amma babu wurin zuwa – Rahama Sadau ta koka
Oladele yace hadarin farko ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a yankin Isaara kusa da Ogere a kan titin Ibadan zuwa Legas da ya rutsa da wata motar Bus kirar Toyota mai lamba AG 346XV.
Hadarin ya kunshi maza biyu a mace daya, inda motar ta kufce madirebanta sakamakon halin maye da yake ciki, wanda yasa ya yi ta gudun wuce sa’a a kan titin har ta kufce masa.
“Hadari na biyu ya faru ne da misalin karfe 11:50 a yankin Fidiwo, kusa da Ogunmakin a kan titin Legas zuwa Ibadan, inda ya rutsa da motar Mazda E2200, shi ma tsananin gudu ya janyo hakan har ya daki wani shinge.
“Maza biyar da mace daya sun samu mummunan rauni, yayin da namiji daya ya mutu nan take. A duka haduran biyu, mun garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.” Inji shi.
Daga karshe Oladele ya gargadi direbobi su kula da dokokin hanya da dokokin tuki musamman yayin da aka fara bude hanyoyi sakamakon sassauta dokokin zaman gida.
A wani labari kuma, akalla mutane 12 wanda yawancin su mata ne aka kashe a garin Oku na karamar hukumar Boki ta jahar Cross Rivers sakamakon zarginsu da ake yi maita da tsafe tsafe.
Guardian ta ruwaito mutanen garin sun lakada ma matan dan banzan duka ne, daga bisani kuma suka cinna musu wuta wanda yayi sanadiyyar mutuwar yawanci daga cikinsu.
Sai dai wata majiya da bata bayyana kanta ba ta bayyana cwa wani babban jami’in gwamnatin jahar Cross Rivers ne ya dauki nauyin kashe mutanen.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng