Ganduje ya saki fursunoni 293 a Kano
A jiya ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya saki fursunoni 293 da ke zaman cin sarka a wani mataki na gyara hali cikin gidajen kaso da ke fadin jihar.
An saki fursunonin masu kananan laifuka bisa ga umarnin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa gwamnatocin jihohi na rage cunkoso a gidajen gyara hali da ke fadin kasar biyo bayan barkewara annobar cutar korona.
Kakakin Hukumar Gidajen Yari ta kasa reshen jihar Kano, DSC Musbahu Lawan Nassarawa, shi ne ba da tabbas a kan wannan lamari na 'yantar da fursunoni kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
DSC Lawan ya shaidawa manema labarai cewa, bayan biyan tara ta kimanin naira miliyan 12 da gwamnan ya yi, ya kuma ba wa kowane daya daga cikin fursunonin da suka shaki iskar 'yanci naira 5,000 kudin komawa gida.
A daya daga cikin gidajen gyara halin da Gwamna Ganduje ya kai ziyara, ya umarci fursunonin da su kasance nagari kuma su yi amfani da wannan dama da aka basu wajen neman na-kai da zai hana su aikata miyagun laifuka.
Kwanturola na Hukumar Gidajen Yari reshen jihar Kano, Mahaji Ahmed Abdullahi, ya yaba da matakan hana yaduwar cutar korona a dukkan gidajen gyara hali na kasa da Kwanturolan Hukumar na kasa, Jafaru Ahmed ya shimfida.
Ya kuma yi godiya tare da yabawa Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje dangane da fadi-tashin da ya ke yi na goyon baya da hadin kai da yake ba wa ma'aikata da fursunoni.
KARANTA KUMA: Sallar Idi: Kano, Katsina da Borno sun yi wa Sarkin Musulmi kunnen uwar shegu
Haka kuma akwai alamu da ke nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya umarci sabon shugaban ma'aikatan fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya soke nade-naden da kuma wasu ayyuka da marigayi Abba Kyari ya amince da su ba tare da izininsa ba.
Duk da shugaban kasar bai bada wani dalili na wannan umarnin ba, amma rahotanni sun bayyana cewa a kalla marigayin ya amince da wasu al'amura 150 ba tare da sanin shugaban kasar ba.
Mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai na shugaban kasa, Femi Adesina ya tabbatar da hakan ga jaridar The Guardian ta sakon kar ta kwana amma kuma ya ki yin tsokaci a kan hakan.
Amma kuma babban mataimakin na musamman ga shugaban kasar a fannin yada labarai, Garba Shehu ya ki mayar da martanin sakon da aka tura masa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng