Ta fasu: Harkallar 781bn ce ta sa aka fatattaki shugaban TCN

Ta fasu: Harkallar 781bn ce ta sa aka fatattaki shugaban TCN

Tsohon manajan daraktan hukumar rarrabe wutar lantarki ta Najeriya (TCN), Usman Gur Mohammed, an sallamesa ne a kan wata badakar wutar lantarki wacce ta kai kimanin dala biliyan biyu, kusan naira biliyan 781, jaridar Daily Trust ta gano.

Takardar sallamar manajan daraktan na dauke da sa hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon shugaban ma'aikatansa, Abba Kyari.

An kuma maye gurbinsa da Injinaya Sule Ahmed Abdulaziz, a matsayin mukaddashin manajan daraktan.

Wannan sallamar ta jawo cece-kuce mai tarin yawa don kuwa har hukumar rarrabe wutar lantarkin tayi zanga-zanga.

Ta fasu: Harkallar 781bn ce ta sa aka fatattaki shugaban TCN
Ta fasu: Harkallar 781bn ce ta sa aka fatattaki shugaban TCN Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Tuni TCN bata da kwamitin zartarwa har zuwa 2014 inda tsohon shugaban kasa Jonathan ya kafa kwamitin mai mambobi 17 karkashin shugabancin Injiniya Haman Tukur a watan Augustan 2013.

An rantsar da Tukur tare da tawagarsa a watan Satumban 2013 amma sai ya yi murabus a watan Janairu 2014 sakamakon wata harkallar N3.85bn.

Har a halin yanzu, tubabben shugaban hukumar rarrabe wutar lantarki da kuma mukaddashin shugaban duk basu samu wasika daga ministan ba.

Hakazalika, an gano cewa tsohon shugaban bai iya cire komai daga ofishinsa ba saboda da karfi da yaji aka fitar da shi yayin da jami'an tsaro suka rako sabon zuwa ofishin.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya soke nade-naden da marigayi Abba Kyari yayi

Amma kuma korarren shugaban TCN din ya ce bashi da masaniya game da wata harkalla da ya toshe kuma bai san maganar wasu kudade ba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Abike Dabiri-Erewa, shugaban hukumar da ke kula da 'yan Najeriya da ke ci-rani a kasashen waje, NIDCOM, a ranar Lahadi sun yi musayar kalamai da Ministan Sadarwa a kan zargin korar maaikatanta daga ofishinsu.

A yayin da Dabiri-Erewa ta zargi Pantami ta rashin mutunta mata, ministan ya mayar da martani inda ya ce babu gaskiya ko kadan a cikin zargin da ta yi.

Rikicin na su ya samo asali ne bayan tsohuwar yar majalisar a cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin NIDCOM a Twitter ta yi ikirarin cewa antami ya bayar da umurnin korar ma'aikatanta daga ofishinsu na Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel