Jerin kasashe 12 da ba a samu bullar cutar korona ba a duniya

Jerin kasashe 12 da ba a samu bullar cutar korona ba a duniya

A halin yanzu da akwai afiye da mutum miliyan 5.3 da bakuwar cutar nan ta coronavirus ta harba cikin nahiyoyi da kasashe 188 a fadin duniya.

Akalla mutum 341,000 sun kwanta dama sanadiyar bakuwar cutar a fadin duniya yayin da kusan mutum miliyan 1.9 suka warke bayan sun kamu kamar yadda alkaluman jami'ar John Hopkins suka fitar.

Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana wannan bakuwa cutar a matsayin annoba wadda ta yi wa duniya kawanya, amma har yanzu akwai wasu nahiyoyi da kasashe da cutar ba ta bulla ba.

Duk da cewa 'Yan Hausa na cewa "daji bai gama ci da wuta ba, ba a yi wa burgu barka", amma a yanzu ana iya cewa akwai wasu kasashe da ba su san da cutar korona ba saboda yadda ba ta kutsa kai cikin su.

Jerin kasashe 12 da ba a samu bulla cutar korona ba a duniya
Jerin kasashe 12 da ba a samu bulla cutar korona ba a duniya
Asali: Twitter

A wani bincike da babbar kafar watsa labarai nan ta Al Jazeera ta gudanar, ta gano cewa akwai wasu kasashe 12 na duniya wanda har kawo yanzu cutar ba ta bulla a cikin su ba.

Kamar yadda binciken ya nuna, mafi sharaha cikin kasashen da cutar ba ta bulla ba ita ce Koriya ta Arewa wadda ke nahiyar Asiya.

KARANTA KUMA: Ganduje ya saki fursunoni 293 a Kano

Babu shakka dai cutar korona ta kutsa kai dukkanin kasashen nahiyar Turai, ba tare da ta rage ko da kasa guda daya ba.

Hakan kuma ta ke a nahiyoyin Amurka ta Kudu da ta Arewa, inda nan ma babu kasar da annobar ba ta mamaye ba.

Ga jerin kasashe 12 na duniya da suka tsarkaka daga cutar korona:

 1. North Korea
 2. Kiribati
 3. Marshall Islands
 4. Micronesia
 5. Nauru
 6. Palau
 7. Samoa
 8. Solomon Islands
 9. Tonga
 10. Turkmenistan
 11. Tuvalu
 12. Vanuatu

A nahiyar Australia, cutar korona ta harbi sama da mutum 6,000, amma har yau ba ta kutsa ba cikin Solomon Islands, Palau, Tuvalu, Nauru, Kiribari, Micronesia, Vanuatu, Tonga da Marshall Islands.

Galibin kasashen nan sun kasance 'yan kananu kuma wadanda su ke a kan tsibiri.

Har yanzu ba sa mu bullar cutar ba a kasar Turkmenistan wadda ita ma ta ke nahiyar Asiya kuma ta hada kan iyaka kasa da Iran, Afghanistan, Uzbekistan da Kazakhstan da cutar ta yi katutu cikin su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel