Da yiwuwar allurar riga-kafin cutar korona za ta samu a karshen watan Yuni

Da yiwuwar allurar riga-kafin cutar korona za ta samu a karshen watan Yuni

- Wata kungiyar ƙwararrun masana kimiyya a Birtaniya su na ci gaba da aiki don samar da rigakafin cutar korona daga yanzu zuwa karshen wata Yuni

- Yayin amfani da wata hanya ta gwajin samun lafiya, ƙwararrun masana su na bincike kan haded-haden wasu magungunan da suka fi tasirin warkar da masu cutar korona

- Cikin magungunan,akwai hydroxychloroquine, lopinavir-ritonavir, da tocilizumab, wadanda su ka ba wa ma su dauke da kwayoyin cutar korona

Kwararrun masana kimiya sun yi hasashen cewa, da yiwuwar za a samar da riga-kafin cutar korona daga yanzu zuwa karshen watan Yunin shekarar da muke ciki.

Masanan su na tsammanin samun tabbaci a kan riga-kafin cutar korona da zarar sakamakon gwajin da suka yi a kan mutane 10,000 masu dauke da kwayoyin cutar ya fito a karshen watan Yuni.

Jaridar The Sun ta kasar Birtaniya ta ruwaito cewa, muddin kwararrun masanan su ka yi nasara a binciken da suka gudanar, to kuwa maganin cutar korona zai tabbata nan ba da dade wa ba.

Yayin amfani da wata hanya ta gwajin samun lafiya, ƙwararrun masanan su na bincike wajen gano hade-haden magungunan da su ka fi tasiri wajen warkar da masu cutar korona.

Da yiwuwar allurar riga-kafin cutar korona za ta samu a karshen watan Yuni
Da yiwuwar allurar riga-kafin cutar korona za ta samu a karshen watan Yuni
Asali: UGC

Babban jagora a kungiyar kwararrun na jami'ar Oxford da ke Ingila, Farfesa Martin Landray, ya ce su na bi sannu-a-hankali wajen gudanar da bincikensu.

Farfesa Landray ya ce da yiwuwar hade-haden wasu magunguna daban-daban ita ce mafificiyar hanyar da za a ci galaba a kan cutar korona kowa ya huta.

KARANTA KUMA: Arzikin Najeriya ya ja baya da kashi 1.87% saboda annobar korona - NBS

Cikin magunguna da kwararrun su ke gudanar da gwaji a kan su domin fidda riga-kafi guda daya sun hadar da; hydroxychloroquine, lopinavir-ritonavir, da kuma tocilizumab.

A yayin da masana kimiya a fadin duniya ke ci gaba da rige-rigen samar da riga-kafin cutar korona, wani kamfanin kera magunguna na kasar Amurka, Moderna, ya cimma wani munzali na nasara.

Kamfanin Moderna mai tushe a jihar Massachusetts ta Amurka, ya kera wani sabon maganin cutar korona, sai dai kuma ya yi gwajin sa ne a kan mutane 'yan kalilan.

Sakamakon gwajin da aka gudanar a kan mutane 45 bayan shan maganin da suke kiran shi da suna mRNA-1273, ya nuna cewa jikinsu ya samu riga-kafin kwayar cutar korona.

A cewar kamfanin Moderna, maganin mRNA-1273, wanda aka kirkira cikin matakai uku na nauyi daban-daban, an baiwa mutane 45 kuma dukkansu sun samu garkuwa da riga-kafin cutar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng