Latest
Rana bata karya, a yau Asabar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP za ta gudanar da taron gangami kuma zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar People's Democratic Party PDP.
Rabiu Musa Kwankwaso ya nesanta kansa da hada-kai da Nyesom Wike wajen samun takara. Kwankwaso ya ce babu abin da ya hada shi da PDP tun da ya bar jam’iyyar.
Jami'an hukumar EFCC sun bayyana cewa sun dira filin wasa na MKO Abiola da ke ABuja ne domin dakile duk wani almubazzanci da yadda ake shakawa deliget kudade.
Fitaccen malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, ya ja kunnen deliget din jam'iyyu da su guji karbar cin hanci wurin zaben 'yan takarar jam'iyyunsu, ba zai kare ba.
Za a ji labari Sanata Oluremi Tinubu za ta hakura da majalisa, yanzu haka akwai mutane hudu da suke neman tikitin APC na yankin tsakiyar Legas a zabe mai zuwa.
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya yi imani da cewa PDP ita ce mafita ga 'yan Najeriya a kan jam'iyya mai mulki (APC) kuma PDP ta fi APC tsoron Allah.
Shugaban kwamitin amintattu na PDP, Sanata Walid Jibril, ya ce duk da cewar jam’iyyar ta yi watsi da tsarin karba-karba, har yanzu akwai damar yin maslaha.
Sanatan yammacin Legas, Solomon Olamilekan Adeola, ya lashe zaben fidda gwanin sanatan da zai wakilci yammacin jihar Ogun a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC.
Masu zafi
Samu kari