Zaben 2023: Jam'iyyar PDP ta fi APC tsoron Allah - Gwamna Fintiri

Zaben 2023: Jam'iyyar PDP ta fi APC tsoron Allah - Gwamna Fintiri

  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa jam'iyyar PDP nesa ba kusa ba ta fi tsoron Allah a kan jam'iyyar APC mai mulki
  • Ya ce duk da jam'iyyar PDP ta tafka kura-kurai a baya ta nemi a gafarta mata, kuma 'yan Najeriya sun yafe mata zunubbanta
  • Ya ce APC sun riga sun dimauce, ya kamata su yi zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam'iyyar gobe amma gashi nan babu wani shiri da suke yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya yi imani da cewa PDP ita ce mafita ga 'yan Najeriya a kan jam'iyya mai mulki (APC) kuma PDP ta fi APC tsoron Allah.

Gwamnan ya zanta da Channels Television a game da gangamin zaben PDP na kasa, wanda ake gabatarwa a ranar Asabar a Abuja. Yayin da ya amince da cewa jam'iyyar ta yi kuskure a baya, amma duk da haka ita PDP ta zarcewa APC.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bayan fita daga PDP, Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour Party

Zaben 2023: Jam'iyyar PDP ta fi APC tsoron Allah - Gwamna Fintiri
Zaben 2023: Jam'iyyar PDP ta fi APC tsoron Allah - Gwamna Fintiri. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC
"Sun riga sun yafe mana sannan ina tunanin ta mu (PDP) ta fi ta su. Mun fi APC tsoron Allah," gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gabatar a Mashood Abiola Stadium Velodrome a Abuja.
"Mun yi kuskure kuma mun roki gafara wanda halin 'dan adam ne. APC na cigaba da tafka kura-kurai sannan duk da haka suna nuna cewa tafarki mai kyau su ke tafiya ga shi 'yan Najeriya na azabtuwa. Mun dade muna lashe raunukanmu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun riga sun daburce

Yayi imani da cewa, da 'yan takara masu nagarta da suka zagaye PDP tare da shirin da jam'iyyar tayi, APC ba za ta zo kusa da jam'iyyarsa ba.

"Idan ka ga dabi'un 'yan takararmu, za ka tabbatar da cewa wannan zaben shugaban kasar na 2023 na wannan jam'iyyar mai daraja ne. APC sun tafka kura-kurai, kuma suna cigaba da yi," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Lafiyarsa lau: Jami'an gidan yari sun magantu kan yanayin da Abba Kyari ke ciki

"Kamar yadda kuke gani sun riga sun daburce. Ya kamata a ce an yi zaben fidda gwanin su gobe. Amma a halin yanzu babu wani shiri daga gare su. Dole tasa INEC duba lamarinsu har ta kara musu kwanaki shida yadda za su samu damar karasa shirye-shiryensu.
"Koma meye sakamakon hakan, ba na tunanin zai tada mana hankula. 'Yan Najeriya sun koyi darussansu kuma a wannan karon PDP suke marawa baya."

Gwamnan, wanda ya bayyana yadda zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben fidda gwanin shugaban kasa, ya bayyana yadda wani 'dan takara ya janye wa 'dan siyasar da aka haifa a Adamawan.

"Hayatu-Deen ya janye masa (Atiku), a cewar Fintiri. Ina ganin ya janye masa. Ya umarci wakilan zabensa da su zabi Atiku," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel