Shugaban kasa a 2023: Atiku ya dauki wasu manyan alkawara, ya caccaki APC

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya dauki wasu manyan alkawara, ya caccaki APC

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a babban zaben kasar mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin hada kan kasar nan
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma dauki alkawarin magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki da ke tunkarar kasar
  • Atiku ya kum yiwa gwamnatin APC wankin babban bargo cewa ta lalata duk wasu nasarori da gwamnatin PDP ta shimfida

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya dauki alkawarin hada kan kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Atiku ya kuma dauki alkawarin tunkarar matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar nan, jaridar Punch ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da jawabin amincewarsa bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP.

Kara karanta wannan

Na yi farin ciki da kasancewa dan takarar PDP a zaben 2023 – Atiku Abubakar

Dan takarar PDP a 2023: Atiku ya sha alwashin yaki da rashin tsaro, ya caccaki APC
Dan takarar PDP a 2023: Atiku ya sha alwashin yaki da rashin tsaro, ya caccaki APC Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Atiku ya caccaki jam’iyyar APC kan yadda ta mayar da nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a lokacin da ta ke rike da madafun iko baya, inda ya yi alkawarin gyara su idan aka sake zabar su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Zan magance matsalolin tsaronmu a kasar nan. Na kuma dauki alkawarin tunkarar matsalolin tattalin arzikinmu. Jam’iyyar PDP ta sanya Najeriya ta zama daya daga kasashe masu ci gaba da wadata a nahiyar Afirka.
“Mun aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka kawo ayyukan yi, da wadata a kasar nan. Jam’iyyar APC ta shigo ta goge duk wadannan nasarori. Shi ya sa na ce yau rana ce mai matukar tarihi. Domin hakan zai ba mu damar gyara duk wani rashin shugabanci na gwamnatin APC.”

Ya kuma nemi hadin kan sauran yan takara a zaben, yana mai cewa babban abun danyawa a gaba shine kwato mulki daga jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar fitar da dan takarar maslaha – Shugaban kwamitin amintattu

Atiku ya ce:

"Bari na yi amfani da wannan damar wajen kira ga abokan takarata. Sannan na basu tabbacin cewa a shirye nake na hada kai da aiki tare da su sannan na basu damar taka rawa a wannan jam'iyyar da gwamnatinmu ta gaba.
“Saboda haka ’yan uwana, ina son in yaba da kokarinku na zurfafa tsarin dimokuradiyya a tsarin wannan jam’iyya. Zaben fidda gwani ne mai inganci. Don haka, na yaba muku akan haka kuma ina fatan yin aiki tare da ku kai da kai. Ta yadda za mu gina wannan jam’iyyar tare zuwa matakin da za mu iya kwace mulki.”

Ya kuma yi kira ga fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar da su ka guji kai al’amuran jam’iyyar kotu.

Na yi farin ciki da kasancewa dan takarar PDP a zaben 2023 – Atiku Abubakar

A gefe guda, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya nuna jin dadinsa a kan lashe zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da ya yi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren

Atiku ya bayyana cewa fafutukar sake gina kasar tare da inganta ta zuwa matakin ci gaba ya fara aiki daga yanzu da ya lashe tikitin takarar shugabancin kasar.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter bayan sanar da nasarar tasa, Atiku ya ce yana duba zuwa ga tattaunawa da yan Najeriya a fadin kasar yayin da suke masu tanadi na musamman saboda gobensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel