Na yi farin ciki da kasancewa dan takarar PDP a zaben 2023 – Atiku Abubakar

Na yi farin ciki da kasancewa dan takarar PDP a zaben 2023 – Atiku Abubakar

  • Bayan nasararsa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya aike sakon murna ga yan Najeriya
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya yi farin ciki sosai da kasancewa wanda zai daga tutar jam'iyyar adawar a zabe mai zuwa
  • Atiku ya kuma bayyana cewa yana duba izuwa ga tattaunawa da al'ummar Najeriya a fadin kasar nan

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya nuna jin dadinsa a kan lashe zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da ya yi.

Atiku ya bayyana cewa fafutukar sake gina kasar tare da inganta ta zuwa matakin ci gaba ya fara aiki daga yanzu da ya lashe tikitin takarar shugabancin kasar.

Na yi farin ciki da kasancewa dan takarar PDP a zaben 2023 – Atiku Abubakar
Na yi farin ciki da kasancewa dan takarar PDP a zaben 2023 – Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Asali: Twitter

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter bayan sanar da nasarar tasa, Atiku ya ce yana duba zuwa ga tattaunawa da yan Najeriya a fadin kasar yayin da suke masu tanadi na musamman saboda gobensu.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar fitar da dan takarar maslaha – Shugaban kwamitin amintattu

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A yau, fafutkar sake ginawa da hade kan kasarmu mai albarka shine kan gaba. Na yi matukar farin ciki da ambata na a matsayin dan takarar jam’iyyar @OfficialPDPNig. Ina duba zuwa ga tattaunawa da yan Najeriya a fadin kasar nan, daukar sakon fata da hadin kai yayin da muke gina makoma daya ga mutane daya.”

A ranar Asabar, 28 ga watan Mayu ne babbar jam'iyyar adawar kasar ta gudanar da zaben fidda dan takararta inda aka fafata tsakanin masu neman kujerar.

Cikakken sakamako: Yadda Atiku ya lallasa Wike, Saraki da sauransu wajen samun tikitin shugaban kasa na PDP

Mun dai kawo cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sake lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Atiku ya samu kuri’u mafi yawa a zaben wanda ya gudana a filin wasa na MKO Abiola a Abuja a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba

Akalla deleget 767 ne suka kada kuri’u domin zartar da hukunci kan makomar masu takarar shugabancin kasar na jam’iyyar adawar da ke fafutukar mallakar tikitin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel