2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

  • Muhammed Dattio, ya lashe tikitin jam’iyyar APC na sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a zaben 2023
  • Dattijo wanda ya kasance kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Kaduna sau biyu ya yi nasara bayan abokan hamayyarsa sun janye
  • Ya kuma nuna karfin gwiwar cewa za su yi nasara a babban zabe mai zuwa saboda nasarorin da gwamnatin El-Rufai ta samu

Kaduna - Muhammed Dattio, tsohon shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kaduna, ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressive Congress(APC) na sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Premium Times ta rahoto.

Mista Dattijo ya lashe zaben ba tare da hamayya ba bayan sauran yan takara biyu da ke neman tikitin jam’iyyar sun janye masa a wajen zaben, kafin a fara kada kuri’a.

Kara karanta wannan

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

Deleget 396 aka tantance domin kada kuri’a a zaben fidda gwanin. A karshen zaben, deleget 388 sun zabi Mista Dattijo yayin da aka soke kuri’u takwas.

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya
2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Hoto: @Dattijo
Asali: Twitter

Yan takara biyu da suka janye masa sune Rabi Salisu da Usman Garba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaben, Dattijo ya mika godiya ga deleget kan karfin gwiwar da suka nuna a kansa da zabarsa don ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa.

Ya ce:

“Ina godiya a gareku ku dukka kan goyon bayan da kuma bani da abokan takara na. za mu yi aiki tare domin nasarar jam’iyyar a babban zabe mai zuwa a watan Fabrairu."

Dattijo zai fafata da Lawal Adamu wanda ya lashe zaben fidda gwani don wakiltan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a babban zaben shekara mai zuwa.

Cikakken sakamako: Yadda Atiku ya lallasa Wike, Saraki da sauransu wajen samun tikitin shugaban kasa na PDP

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sake lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Atiku ya samu kuri’u mafi yawa a zaben wanda ya gudana a filin wasa na MKO Abiola a Abuja a ranar Asabar, 28 ga watan Mayu.

Akalla deleget 767 ne suka kada kuri’u domin zartar da hukunci kan makomar masu takarar shugabancin kasar na jam’iyyar adawar da ke fafutukar mallakar tikitin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel