Da duminsa: Sanatan Legas ya ci zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Ogun

Da duminsa: Sanatan Legas ya ci zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Ogun

  • Sanatan yammacin Legas, Solomon Olamilekan Adeola, ya lallasa abokin hamayayyarsa kuma babban abokin adawarsa da a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC na sanatan da zai wakilci yammacin jihar Ogun
  • Da farko dai, abokin hamayayyarsa, wanda shi ne sanatan dake wakiltar yammacin Ogun, Tolu Odebiyi, ya fara cika baki ganin yadda 'yan takara biyu suka janye masa, hakan yasa ya samu tabbacin karo kujerarsa
  • Hakan yasa ya kira Olamilekan da "bako" wanda yazo kawo musu ziyara duba da ba 'dan asalin jihar bane, sai dai ba anan gizo ke saka ba, abokin hamayayyar nasa ya lallasa shi tare da kwashe dukkan kuri'un ba tare da ya tsira da ko guda ba

Ogun - Sanatan yammacin Legas, Solomon Olamilekan Adeola, ya lashe zaben fidda gwanin sanatan da zai wakilci yammacin jihar Ogun a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

Adeola wanda aka fi sani da Yayi ya samu kuri'u 294 inda ya lallasa babban abokin hamayayyarsa sannan sanata mai wakiltar yankin, Tolu Odebiyi, wanda bai tsira da ko kuri'a daya ba.

Da duminsa: Sanatan Legas ya ci zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a Ogun
Da duminsa: Sanatan Legas ya ci zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a Ogun. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya lashe zaben fidda gwanin sanatan da ya gabata a dakin taron Orona, na Ilaro, hedkwatar karamar hukumar Yewa na jihar, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Sanatan dake wakiltar yankin yammacin Legas din bai dade da dawowa jihar ba, tare da fara neman takarar sanatan yammacin Ogun, a wani tsarin siyasa mai taken "West2West Agenda."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamitin tsara zaben jam'iyyar APC ce ta gabatar da zaben fidda gwanin karkashin jagorancin Dr Dapo Odukoya.

Da farko, Odebiyi ya ce shi kadai ne 'dan takarar jam'iyyar APC na fidda gwani a yankin.

Odebiyi, sirikin tsohon gwamna, Amosun, ya isa wajen zaben misalin karfe 12:48 na rana tare da wasu daga cikin mabiyansa.

Kara karanta wannan

Sunayen jihohi da 'yan takarar gwamnoni da suka yi nasarar samun tikitin APC a zaben fidda gwani

Yayin zantawa da manema labarai, Odebiyi ya shaida cewa shi kadai ne 'dan takara a zaben fidda gwanin.

Ya siffanta abokin hamayayyarsa na jihar Legas a matsayin "bako" a wurin.

Ya cigaba da bayyana yadda dukkan sauran abokan takarar nasa guda biyu - Hon. Abiodun Isiaq Akinlade da wanda ya yi takarar gwamnan jihar sau uku, Prince Gboyega Nasiru Isiaka (GNI) suka janye masa tuntuni don su yi takarar 'yan majalisu.

A cewarsa: "Ina matukar murnar yadda daga karshe muka samu damar da zamu gudanar da zaben fidda gwanin mu, babban abu ma ina matukar ta ya mutanen yammacin Ogun murna.
"A wuri na, ba na tunanin ina da abokin hamayya a wannan karon. Ni kadai ne 'dan takarar yammacin Ogun.
"'Yan uwana guda biyu - Isiaka Abiodun Akinlade da Gboyega Nasiru Isiaka - wadanda 'yan asalin yammacin Ogun ne sun amince da komawa takarar 'yan majalisu.
"A wurina, ni kadai ne 'dan takarar yammacin Ogun. Eh, muna da bako (Yayi) wanda ya zo wurinmu. Za mu bashi masauki gami da jin ta bakinsa, sannan daga karshe, na yi imani ni ne zanyi nasara."

Kara karanta wannan

Babu banbancin tsakanin Deleget da dan bindiga mai karbar kudin fansa, Shehu Sani

Asali: Legit.ng

Online view pixel