Burundi: An Samu Gawar Minista a Mota, an Masa Mummunan Rauni a Kai
- Ministan sadarwa na kasar Burundi, Gabby Bugaga ya rasu a wani yanayi mai cike da sarkakiya da ake cigaba da ce-ce-ku-ce game da shi
- Rahoto ya nuna cewa gwamnatin kasar ta tabbatar da rasuwar Gabby Bugaga, inda ta ce ya mutu ne sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi
- Yayin da wasu ke nuna shakku kan dalilin rasuwarsa, wasu rahotanni sun nuna cewa an yi masa mummunan rauni a kayi kuma an fasa motarsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Burindi - Wani minista a kasar Burundi ya rasu a wani lamari da gwamnati ta bayyana a matsayin hatsarin mota, yayin da wasu majiyoyi suka ce har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar ba.
An gano gawar Gabby Bugaga a cikin wata mota kirar 4x4 da manoma suka tarar, kusan mita 10 daga wata hanya da ba a cika amfani da ita ba kuma ake kallonta a matsayin mai hadari.

Kara karanta wannan
Ana shirin tafiya Hajji, an fara barazanar tsayar da aiki da jiragen sama a Najeriya

Source: Twitter
Rahoton Reuters ya nuna cewa an same shi ne a wata hanyar da ake bi ta cikin gonakin dabino a yankin Kivoga, kimanin kilomita 10 a Arewa da cibiyar tattalin arzikin kasar, Bujumbura.
Yadda aka samu gawar ministan
Wasu majiyoyi biyu sun tabbatar da hotunan gawar, inda aka gan shi ya fadi gefe a kujerar direba cikin motar da ta lalace, bayan manoma sun wallafa hotunan a shafukan sada zumunta ba tare da sun gane shi ba.
Gwamnatin Burundi ta ce:
“Gwamnatin Jamhuriyar Burundi na bakin cikin sanar da rasuwar ministan sadarwa da kafafen yada labarai, Gabby Bugaga, wanda ya rasu da safiyar ranar 16 ga Afrilu, 2026 sakamakon hatsari,”
Rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa kakakin gwamnatin kasar, Jerome Niyonzima ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani ba.
Bayanin da 'yan sanda suka yi
Tun da farko, wata majiya daga ‘yan sanda ta tabbatar da cewa gawar da aka samu ta ministan ce kamar yadda wasu rahotanni suka nuna.
“Har yanzu ba a tantance musabbabin mutuwarsa ba,”
In ji majiyar, tana mai cewa Bugaga ya samu “mummunan rauni a kansa,” yayin da bangaren dama da bayan motar suka lalace sosai.

Source: Twitter
Majiyar ‘yan sandan ta ce rasuwar ministan na dauke da tambayoyi da dama da ba su da amsa, tana mai cewa duk da raunin da ya samu a kayi:
“Cikin motar bai lalace ba, kuma me ya sa babu alamun hadari a gaban motar?”
Ta kara da cewa:
“Gwamnati ta yanke shawarar rufe lamarin ba tare da bincike a hukumance ba.”
Sai dai wani jami’in gwamnati, wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar ministan.
Halima Sabuwa ta rasu a Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa an sanar da rasuwar jarumar Kannywood da aka fi sani da Halima Sabuwa bayan fama da jinya.

Kara karanta wannan
Akwai gagarumar matsala, Iran ta sanar da asarar da ta tafka a yakin Amurka da Isra'ila
Tun kafin rasuwarta, jarumar ta bayyana a wani bidiyo tana neman taimakon al'umma, inda ta sanar da cewa damuwar duniya ta mata yawa.
Jaruman Kannywood da sauran jama'a sun yi tururuwar mata addu'a kuma an mata sallar jana'iza a jihar Kano kamar yadda Musulunci ya tanada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
