Bayan janye takara, Sanatan APC ya sauya sheka daga jam'iyyar zuwa PDO

Bayan janye takara, Sanatan APC ya sauya sheka daga jam'iyyar zuwa PDO

  • Sanatan Kebbi ta tsakiya kuma tsohon ministan Abuja, Sanata Adamu Aleiru ya suaya sheka daga APC zuwa jam'iyyar PDP
  • Da farko dai Sanatan ya tsame kansa daga zaɓen fitar da ɗan takarar Sanatan APC, inda ya zargi cewa an shirya magudi da damfara
  • Gwamna Kebbi, Atiku Bagudu, shi ne ya lashe tikitin takarar sanatan bayan Aleiru ya janye, hakan ya ba shi nasara ba tare da hamayya ba

Kebbi - Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya a majalisar Dattawa ta ƙasa, Sanata Adamu Aleiru, ya yanje daga tseren neman tikitin tazarce kan kujerarsa a APC.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa bayan haka Sanatan ya sauya sheƙa daga APC zuwa babbar jam'iyyar hamayya wato PDP.

Sanata Adamu Aleiru.
Bayan jnaye takara, Sanatan APC ya sauya sheka daga jam'iyyar zuwa PDP Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Babban mai taimaka masa ta bangaren yaɗa labarai, Abdullahi Zuru, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ta wayar salula.

Kara karanta wannan

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

A kalamansa, Zuru ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Eh dagaske ne, Aleiru ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP, amma yanzun ina taro ne, zan kira ku daga bayan idan na gama."

Meyasa ya ɗauki wannan matakin?

Tun da farko dai, tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja ya tura takarda ga shugaban APC na ƙasa, inda ya sanar da shi matakin da ya ɗauka na kauracewa zaɓen fid da gwani.

Aleiru ya yi zargin cewa gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya canza ainihin Deleget ya maye gurbin su da wasu daban, wannan dalilin ya sa ya tsame kansa daga abin da ya kira abun kunya da shirin damfara.

A wani labarin na daban kuma Mako ɗaya bayan Murabus, Ministan Buhari ya lashe tikitin gwamna a APC

Tsohon ministan haƙar ma'adanai da ƙarafa, Uche Ogah, bai rasa baki ɗaya ba bayan ya yi murabus daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mako ɗaya bayan Murabus, Ministan Buhari ya lashe tikitin gwamna a APC

A ranar 27 ga watan Mayu, 2022 aka bayyana Ogah a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Abia na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel