Yan bindiga sun kashe ango, sun sace wasu da dama harda iyalan tsohon kwamishina a Kaduna

Yan bindiga sun kashe ango, sun sace wasu da dama harda iyalan tsohon kwamishina a Kaduna

  • Yan bindiga su fiye da 50 sun kai hari garin Jere a karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, a ranar Asabar
  • Maharan sun kai hari gidan wasu sabbin ma'aurata inda suka kashe angon sannan suka sace wasu mutane da yawa
  • Daga cikin wadanda aka bi gida-gida aka sace harda iyalan tsohon kwamishinan yaki da talauci na jihar su hudu

Kaduna - Wasu tsagerun yan bindiga a safiyar ranar Asabar, 28 ga watan Mayu, sun farmaki garin Jere a karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, inda suka kashe mutum daya tare da sace wasu da dama ciki harda mutum hudu yan gida daya.

An tattaro cewa yan bindigar sun kashe wani sabon ango sannan suka yi awon gaba da matarsa wacce ke dauke da juna biyu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ƴan Ta'adda Sun Bindige Ango Har Lahira, Sun Sace Amaryarsa Mai Juna Biyu a Kaduna

Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu mutum hudu a ahlin Abdulrahman Ibrahim Jere, tsohon kwamishinan yaki da talauci a jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Yan bindiga sun kashe ango, sun sace wasu da dama a Kaduna
Yan bindiga sun kashe ango, sun sace wasu da dama a Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar wata majiya, yan bindigar da suka farmaki garin sun fi guda 50 kan babura, inda suka shiga gida-gida don aiwatar da ta’asarsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyar ta ce:

“Mun kasa bacci. Yan bindigar sun zo da yawansu a kan babura kowannensu dauke da muggan makamai sannan suka bi gida-gida.
“Amma sun tunkari gidan tsohon kwamishina inda suka sace matarsa, yarinya karama, kanwa da surukarsa."

Majiyar ta kara da cewar yan bindigar sun farmaki gidan wasu sabbin ma’aurata inda suka harbe angon da ya turje sannan suka sace matarsa, rahoton The Eagle.

An tattaro cewa harin ya tunzura mazauna yankin, musamman matasa wadanda suke ganin cewa hare-hare na gudana duk da kasancewar jami’an tsaro. Sun yi al’ajabin ta ydda yan iska za su iya aiki tsawon awa uku ba tare da cikas ba.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, IPOB Ta Bayyana Abin Da Ta Sani Game Da Kisar Gillar Da Aka Yi Wa Harira Da 'Yayanta 4 a Anambra

Ya kara da cewar bayan awannin da kai harin, jami’an tsaro sun bayyana sannan suka yi ikirarin kashe yan bindiga biyu.

Rundunar yan sandan jihar Kaduna bata riga ta tabbatar da lamarin ba don ba a samu jin ta bakin kakakinta, Mohammed Jaluge ba.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina

A wani labarin, tsagerun yan bindiga sun kashe akalla mutane 12 a kauyen Gakurdi da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, Channels TV ta rahoto.

Yan ta’addan sun kona gonaki da dama mallakar mazauna kauyen a yayin farmakin sassafe da suka kai yankin wanda ya shafe tsawon awanni.

Wani ganau ya shaidawa gidan talbijin na Channels cewa maharan dauke da muggan makamai sun isa kauyen ne a kan babura sannan suka fara harbi kan mai uwa da wabi don tarwatsa al’ummar garin.

Kara karanta wannan

An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel