Taliyar karshe: Jiga-jigan APC za su karbe kujerar Mai dakin Tinubu a Majalisar Dattawa

Taliyar karshe: Jiga-jigan APC za su karbe kujerar Mai dakin Tinubu a Majalisar Dattawa

  • Oluremi Tinubu ba za ta koma majalisar dattawa ba, a 2023 za ta cika shekara 12 a kujerar Sanata
  • Kusan doka ce a jam’iyyar APC ta Legas, mutum ba zai yi shekara da shekaru yana rike da kujera ba
  • Sanata Tinubu za ta ba wani wuri yayin da mijinta, Bola Tinubu yake yin takarar shugaban kasa

Lagos - Sanata Oluremi Tinubu watau uwargidar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu za ta bar majalisar dattawa saboda burin mai gidanta na zama shugaban kasa.

Jaridar Daily Trust ta ce Oluremi Tinubu ba za ta shiga zaben zama ‘yar takarar jam’iyyar APC na kujerar Sanata wanda za a gudanar a karshen makon nan ba.

Hakan ya yi sanadiyyar da wasu ‘yan siyasan Legas ta tsakiya sun fara harin kujerar Sanatar a 2023.

Kara karanta wannan

Halin da Atiku, Saraki, Tambuwal, da Wike suke ciki a wajen zaben zama ‘dan takaran PDP

Tim 2011 uwargidar tsohuwar gwamnan na jihar Legas ta ke majalisa, a Mayun 2023 za ta cika shekaru 12 ta na rike da kujerar Sanata, ta yi wa’adi har uku.

Al'adar Sanatocin Legas

Rahoton ya ce sauran Sanatocin Legas sun yi shekaru hudu ko takwas ne a kujerunsu. A kan Oluremi Tinubu ne aka samu wanda ta zarce har sau biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanata Gbenga Ashafa wanda ya wakilci Legas ta gabas ya yi wa’adi biyu tsakanin 2011 da 2019. A zaben 2019 ne ya rasa tikitin APC a hannun Bayo Osinowo.

Mai dakin Tinubu
Remi Tinubu da Bola Tinubu Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Bayan rasuwar Bayo Osinowo, sai aka zabi Tokunbo Abiru. Masu nazarin siyasa su na cewa akwai wata doka da ba a rubuta ba da ta kayyade takara a Legas.

Masu neman Sanatan Legas ta tsakiya

Akwai mutane hudu masu neman tikitin APC na Legas ta tsakiya. Daga ciki har da tsohon Ministan tsaro da tsohon mataimakin shugaban majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar Arewa

Hon. Wasiu Eshinlokun da Demola Seriki sun nuna sha’awar tsayawa zaben tsaida gwani a APC.

Sannan shugaban tafiyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (ABAT) watau Hon. Oyinlola Danmole da Hon. Akeem Apatira duk sun ci burin takarar Sanatan a zaben 2023.

Dukkanin masu neman takarar sun dage da kamfe bayan jin cewa Tinubu ta na goyon bayan Wasiu Eshinlokun ya samu tikiti domin yam aye gurbinta a majalisa.

Tazarcen Gwamnoni a 2023

A baya kun ji labari cewa Dapo Abiodun, Ahmadu Fintiri, Bala Mohammed, AbdulRahman AbdulRasaq su na cikin gwamnonin da sai sun dage a zaben 2023.

Hasashen mu ya na nuna mana zai yi wahala a karbe mulki a hannun Mai Mala Buni, Babajide Sanwo-Olu, da kuma Gwamnam jihar Borno, Babagana Umara Zulum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel