Kwankwaso ya yi magana a kan zargin yi wa Wike ko wani ‘dan takara aikin boye a PDP

Kwankwaso ya yi magana a kan zargin yi wa Wike ko wani ‘dan takara aikin boye a PDP

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya nesanta kansa da zargin hada-kai da Nyesom Wike wajen samun takara
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce babu abin da ya hada shi da PDP tun da ya bar jam’iyyar kwanaki
  • Tsohon Gwamnan Kano zai shigar da kara a kan gidan yada labaran da suka ce ya karbi wasu Daloli

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso ya musanya zargin da yake yawo na cewa ya karbi kudi daga hannun Nyesom Wike mai neman takarar shugaban kasa.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce zargin cewa Nyesom Wike ya ba shi $15, 000 a kan kowane mai zaben ‘dan takarar shugaban kasa na PDP ba gaskiya ba ne.

Hadimin ‘dan takarar shugaban kasar, Ibrahim Adamu ya bayyana haka a wani jawabi na musamman da ya fitar a yammacin yau, 28 ga watan Mayu.

Adamu ya yi wa jawabin da ya fitar a Facebook take da ‘Press Release on Alleged Sen. Kwankwaso’s Involvement in Governor Wike’s Presidential Ambition.’

Magana za ta je gaban kotu

A jawabin, ‘dan siyasar ya nuna babu gaskiya ko na sisin kobo a labarin da ake yadawa. Baya ga kira ayi watsi da labarin, Kwankwaso zai kai kara a kotu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har ila yau, jawabin da aka fitar ya ce an fito da wannan labarin bogi ne da nufin kurum a bata masa suna, a kuma ci mutuntin tsohon Sanatan na Najeriya.

Kwankwaso da Wike
Tsohon hoton Sanata Rabiu Kwankwaso da Nyesom Wike Hoto: silvernewsng.com
Asali: UGC

“Wannan labari, wanda sam ba gaskiya ba ne, yana cewa Sanata kuma Jagoran jam’iyyar NNPP ya karbi $15, 000 daga wajen Nyesom Wike, ya killace masu zaben ‘dan takara a PDP, kuma ya killace su a wani otel.”

“Sanannen abu ne cewa a ranar 29 ga watan Maris 2022, Mai girma Sanata Mohammed Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP.”
“Mun karyata wannan labari kaco-kam dinsa, kuma mu na kira ga mutane su yi watsi da shi a matsayin kanzon kuregen kafar yada labaran zamani.”
“Mu na kira ga wannan kafar labarai ta yanar gizo, ta janye wannan labari na karya, sannan kuma ta nemi afuwa a manyan jaridun kasa guda uku.”

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kira ga maboya bayansa

Tsohon Ministan tsaron ya nemi mutane su yi watsi da labarin domin bai da tushe ko makama.

“A karshe Sanata Kwankwaso yana kira ga dinbin mabiya da magoya bayansa da su jajirce; domin za a rika kawo irin wadannan labaran karya lokaci bayan lokaci.”

- Rabiu Musa Kwankwaso

Sanata Kwankwaso ya ce an sanar da lauyoyinsa game da wannan labari da zai bata sunansa, kuma zai shigar da kara a gaban kotu a kan gidan yada labaran.

Yadda za ta kaya a zaben PDP

Ku na da labari cewa Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya fito neman takarar kujerar shugaban kasa a PDP gadan-gadan, zai gwabza da su Atiku Abubakar.

Ana tunanin Nyesom Wike yana da kudin da zai iya kashewa wajen samun tikiti, sannan ya sha gaban duk masu harin zama ‘dan takara daga yankin Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel