Latest
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da tsohon shugaba da ma’ajin ABU a gaban babban kotun jihar Kaduna kan zargin wawure kudi har biliyan daya.
Wasu direbobi a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kano sun rufe hanya sakamakon halaka abokin aikinsu da wani Soja yayi a Tashar Yari da ke karamar hukumar Makarfi.
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana matsayarta game da yadda take shirin yin zaben 2023. Ta ce bata taba tunanin dage zabe ba, don haka za a yi zabe.
Rundunar yan sandan jihar Katsina a ranar Laraba, 11 ga watan Janairu ta tabbatar da kama wasu matasa uku kan zargin sace yarinya yar shekara shida a Kano.
Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya shafe kwana da kwanki ba a san inda ya shiga ba sai jiya ya dawo, Emefiele ba zai dade ana Najeriya ba zai sake lulawa kasar waje
Alkalin alkalai na jihar Oyo, Munta Abimbola ya saki wata dattijuwa yar shekara 65 da jikanta dan shekara 15 da aka tsare a gidan yari kan satar kaji 2 a Oyo.
Wata lakcara a jami'ar Nnamdi Azikiwe ta jihar Anambra, ta haifa yara bakwai reras. Mijinta yayi kira ga jama'ar Annabi da su tallafa musu saboda jariraan.
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya kaddamar da yakin neman zaben APC a Benuwai, yana ganin sauya-shekar da Gwamna Samuel Ortom tamkar sace masu kuri'a ne.
Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari sakatariyar karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra inda suka halaka yan bijilante uku sannan suka kona wasu gine-gine.
Masu zafi
Samu kari