Gwamna Badaru Ya Caccaki Tsohon Mataimakin Gwamna Da Ya Koma PDP a Jigawa

Gwamna Badaru Ya Caccaki Tsohon Mataimakin Gwamna Da Ya Koma PDP a Jigawa

  • Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru, ya maida martani ga tsohon gwamnan jihar da ya sauya sheka zuwa PDP
  • Ahmad Mahmoud, ya rike kujerar mataimakin gwamna a zamanin mulkin Sule Lamido daga 2007 zuwa 2015
  • Sai dai a yan kwanakin da suka shuɗe, Mahmoud ya tattara kayansa daga APC kuma ya soki mulkin Badaru

Jigawa - Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa ya caccakin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Ahmad Mahmoud, wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa gwamna Badaru, mamba a jam'iyyar APC ya kira tsohon gwamnan da makaryaci wanda bai kamata a amince masa ba.

Taron kamfen APC a Jigawa.
Gwamna Badaru Ya Caccaki Tsohon Mataimakin Gwamna Da Ya Koma PDP a Jigawa Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin gangamin ralin APC da ya gudana a karamar hukumar Sule Tankarkar, Jigawa, daya daga cikin jihohin arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam'iyya Ta Maye Gurbinsa

Meyasa tsohon gwamnan ya bar APC?

Mista Mahmoud a wata wasika da ya aike wa shugaban APC na gundumar Galagamma, karamar hukumar Gumel, yace ya yanke fita daga jam'iyya mai mulki ne saboda ba ta shriya lashe zaben 2023 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mataimakin gwamnan ya shiga PDP ne a wani taro na musamman da aka shirya a gidan Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar dake Bamaina, karamar hukumar Birnin Kudu.

A ruwayar Dailypost Mista Mahmoud ya ce:

"Na kan zubda hawaye a duk lokacin da naga abinda ke faruwa a APC kuma na tuna yadda abubuwa suke lokacin muna gwamnatin PDP."
"Ni da magoya bayana da muka kai APC ga nasara a 2015 da 2019 mun fice daga inuwarta kuma zamu yi aiki tukuru domin dawo da PDP kan madafun iko a 2023."

Gwamna Badaru ya maida martani

Kara karanta wannan

Tinubu Ko Atiku: An Tona Sunan Dan Takarar da Kwankwaso da Peter Obi Suke Wa Aiki a Zaben 2023

Da yake martani kan kalaman tsohon mataimakin gwamna, Badaru yace Mahmoud ya shirga karyane kawai. Ya kuma yi ikirarin cewa tsohon mataimaki ya bar APC ba tare da amincewar mutanen Gumel ba.

Badaru ya ce:

"Na yaba da mutanen Gumel bisa rashin mara masa baya zuwa inda ya koma yanzu. Wannan mutum ne da zai iya rantsewa da Alƙur'ani kan karya."
"Ina fatan Allah ya tona masa asiri, ya saba kirkirar ƙarya a kaina da mataimaki na, muna Addu'a Allah ya bayyana gaskiya Asirinsa ya tonu."

A wani labarin kuma Watanni Bayan Dan Takarar Gwamna Ya Mutu, PRP Ta Maye Gurbinsa a Ogun

Watanni hudu bayan rasuwar dan takarar gwamnan jihar Ogun, jam'iyyar PRP ta maye gurbinsa da Cyrus Johnson.

Allah ya yi wa tsohon dan takarar, David Bamgbose, rasuwa a watan Satumba bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel