Direbobin Tanka Sun Kulle Hanyar Zaria zuwa Kano Kan Kisan Abokin Aikinsu

Direbobin Tanka Sun Kulle Hanyar Zaria zuwa Kano Kan Kisan Abokin Aikinsu

  • Wasu fusatattun direbobin motocin mai sun tsare titin Zaria zuwa Kano na tsawon awanni a matsayin zanga-zanga bayan bindige abokin akinsu da soja yayi
  • Lamarin da ya auku kusa da Tashar Yari dake karamar hukumar Makarfi ya biyo bayan wata hatsaniya da ta shiga tsakanin sojan da direban motar man wani kamfanin kwangilar
  • Sai dai, ba a gama gano musabbabin rikicin ba, amma hukumomin tsaro suna kan binciken lamarin, inda rundunar soji ta kama wanda ake zargin

Kaduna - An fuskanci tashin hankali kan babban titi Zaria zuwa Kano yayin da direbobin motocin mai suka tsare titin bayan wani soja ya halaka abokin aikinsu.

Taswirar Kaduna
Direbobin Tanka Sun Kulle Hanyar Zaria zuwa Kano Kan Kisan Abokin Aikinsu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An gano yadda lamarin ya auku misalin karfe 3:30 na ranar Laraba yayin da fusatattun direbobin suka tsare babban titin tare da tsaida ababen hawa a titin dake cike da zirga-zirga tsawon awanni.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Cigaba da Yin Rabon Mukamai, Ya Nada Sabon Shugaban FHFL

Daily Trust ba iya gano mahadin sojan da kamfanin kwangilar da marigayin direban.

Sai dai, an tattaro yadda lamarin ya auku kusa da Tashar Yari a karamar hukumar Makarfi dake jihar Kaduna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin tabbatar da toshe hanyar da fusatattun direbobin dake zanga-zanga sukayi da kuma kisan direban, shugaban hukumar kula da tsare titina na rikon kwaryar yankin, Lawal Garba ya ce an tuntubi sauran hukumomin tsaro don taimakawa wajen shawo kan lamarin gami da bude babban titin ga masu ababen hawan da jigata.

"An fara toshe titin ne bayan sojan dake aiki a kamfanin kwangilar wanda ke aiki kan titin ya harbe wani direban motar mai bayan wata hatsaniya. Direbobin motar man suka toshe titin gaba daya a matsayin zanga-zanga.
"Na tuntubi daraktan DSS, kwamishinan 'yan sanda da na NURTW. Haka zalika, na sanarwa daraktan kula da tsaron cikin gida game da lamarin. Muna kokarin ganin an shawo kan matsalar."

Kara karanta wannan

FG Ta Magantu Kan Yuwuwar Fasawa ko Dage Zaben 2023 Mai Gabatowa

- A cewarsa.

Har ila yau, Daily Trust ta tattaro yadda rundunar soji ta kama wanda ake zargin.

Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce kwamishinan 'yan sanda, Yekini Ayoku, yayi umarni da binciken lamarin.

Yan bindiga sun halaka jami’an NSCDC a Birnin Gwari

A wani labari na daban, wasu miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki a yankunan Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

An gano cewa sun halaka jami’an NSCDC bakwai a farmakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel