Tafiyar Peter Obi Ta Samu Tagomashi A Kaduna Yayin Da Mataimakin Kakakin Majalisa, Mamba Suka Bar APC Zuwa LP

Tafiyar Peter Obi Ta Samu Tagomashi A Kaduna Yayin Da Mataimakin Kakakin Majalisa, Mamba Suka Bar APC Zuwa LP

  • A karon farko a jihar arewa, an samu jiga-jigai daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Labour
  • Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Isaac Auta Zankai da mamba mai wakiltar mazabar Zaria, Suleiman Dabo ne suka bude wannan fagen
  • Umar Farouk Ibrahim, shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour ya sanar da sauya shekansu a Kaduna

Jihar Kaduna - Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Isaac Auta Zankai da mamba mai wakiltar mazabar Zaria, Suleiman Dabo, sun fita daga jam'iyyar APC sun koma Jam'iyyar Labour, LP, The Punch ta rahoto.

Mataimakin kakakin majalisar shine ke wakiltar yankin Kauru a majalisar jihar.

Kaduna Map
Tafiyar Peter Obi Ta Samu Tagomashi A Kaduna Yayin Da Mataimakin Kakakin Majalisa, Mamba Suka Bar APC Zuwa LP. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Sakataren jam'iyyar Labour na kasa kuma ciyaman din kwamitin takarar gwamna, Umar Farouk Ibrahim ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da mambobin kwamitin kamfen din gwamna da gabatar da manufofinsu a ranar Alhamis a Kaduna.

Kara karanta wannan

2023: Magana Ta Kare, Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Ana Gab da Zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim ya cika baki da cewa rabin mambobin majalisar mabiya tafiyar "Obi-Datti" ne, yana mai cewa karbuwar da jam'iyyar ta samu a jihar da kasa alama ce da ke nuna za su yi nasara a zaben da ke tafe.

Ya ce:

"Maganar gaskiya, yau na daya cikin ranakun mafi farin ciki a rayuwa ta. Na fita yin kamfen ga dan takarar shugaban kasarmu Peter Obi kuma an tarbe ni sosai.
"Na gamsu da irin mutanen da suka halarci kaddamarwar. A dukkan jihohin arewa ba mu da yan takarar da suka fita daga APC zuwa Jam'iyyar Labour sai Kaduna inda mataimakin kakakin majalisa da mamba mai wakiltar Zaria suka sauya sheka."

Jigon na LP ya bukaci yan jam'iyyar su hada kai domin ganin sun samu nasara a babban zaben da ke tafe.

Ya shawarci matasan Najeriya, wadanda sune suka fi yawa a jam'iyyar ta LP kada su yi kasa a gwiwa har sai Obi da Datti sun kafa gwamnati na gaba a kasar don a cewarsa 'mulki na hannun matasa.'

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Atiku da Peter Obi Sun Shiga Matsala, Sun Yi Gagarumin Rashi Ana Gab Da Zabe

Yar Takarar mataimakin gwamna ta fita daga APC ta koma PDP

A wani rahoton, Mrs Helen Boco, yar takarar mataimakin gwamna a jihar Rivers a zaben 2023 karkashin inuwar jam'iyyar APC ta sauya sheka zuwa PDP.

Kamar yadda jaridar Tribune ta rahoto, an samu wannan cigaban ne ana kwanaki 49 kafin zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel