Faston Da Ya Kware a Sukar Buhari Ya Fadi Abin da Hadimin Shugaban Kasa Ya Fada Masa

Faston Da Ya Kware a Sukar Buhari Ya Fadi Abin da Hadimin Shugaban Kasa Ya Fada Masa

  • Ga dukkan alamu musayar yawu da ake yi tsakanin fadar shugaban kasa da babban Bishop na Sakkwato, Mathew Kukah, ba mai karewa bane
  • Malamin addinin dai ya bayyana cewa aikinsa ne sukar masu rike da madafun iko don amfanin al'umma
  • Kukah ya ce sun hadu da Femi Adesina, kakakin shugaban kasa Buhari a fadar villa har suka yi yar zantuka a tsakaninsu

Babban Bishop na Sakkwato, Mathew Kukah, ya bayyana abun da suka tattauna da mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman a kafofin watsa labarai, Femi Adesina.

A wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV, Kukah ya ce shi mutum ne mai fadar gaskiya ga mutanen da ke rike da madafun iko.

Adesina da Kukah
Faston Da Ya Kware a Sukar Buhari Ya Fadi Abin da Hadimin Shugaban Kasa Ya Fada Masa Hoto: Guardian, The Punch
Asali: UGC

Hirar malamin addinin na zuwa ne yan kwanaki bayan ya zargi gwamnatin Shugaba Buhari da nuna son kai da kuma gaza cika alkawaran da ta daukarwa al'ummar kasar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Ainihin Manufar Ƙirƙirar Ƙungiyar Boko Haram

Da yake martani ga malamin, Adesina ya ce Bishop Kukah ya gaza sauke hakkin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na mai fada aji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, bayan ziyarar da ya kai fadar shugaban kasa, Kukah ya ce ya yi yar gajeriyar hira da Adesina.

Ya ce:

"A kodayaushe ina fada ma mutane cewa magana ta gaskiya, bana damun kaina a kan suka saboda ina kallon kaina a matsayin malami. Ban taba yin fushi ba idan wani ya nuna bai aminta da ni kan wani abu ba.
"Femi na da aikin yi, ana biyansa don yin aikin. Ina da nawa aikin. Amma babu wani abun san zuciya a ciki. Ina karanta sukarsu da dama; ba sa damuna saboda wasun su kamata ya yi su kauce ma abun da na fadi."

Da yake ci gaba da magana, malamin ya ce ya karanta jawabin Adesina kuma baya tunanin akwai bukatar yin martani.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

Ya kara da cewa:

"Na karanta jawabinsa, bana tunanin akwai wani dalili da zai sa ni mayar da martani ga abun da suka fadi. Kuma na tuna haduwar karshe da muka yi a Villa, Femi ya ce mani cikin barkwanci 'Bishop kana sukar gwamnatina a koda yaushe; don haka ka zo yau.
"Na fada masa ina sukar gwamnati kafin zuwanka kuma zan soki gwamnati bayan tafiyarka."

Na cika alkawaran da na daukarwa al'ummar Najeriya, Buhari

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewar lallai ya cika dukkanin alkawaran da ya daukarwa al'ummar kasar kama daga murkushe Boko Haram, bunkasa tattalin arziki da kuma yakar cin hanci da rashawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel