An Gurfanar da Tsohon Shugaban ABU Da Ma'ajin Jami'ar Kan Zargin Damfarar N1bn

An Gurfanar da Tsohon Shugaban ABU Da Ma'ajin Jami'ar Kan Zargin Damfarar N1bn

  • Hukumar EFCC reshen jihar Kaduna ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba a gaban kotu
  • EFCC ta kuma gurfanar ma'ajin jami'ar ta ABU, Ibrahim Shehu Usman, a gaban alkalin babbar kotun jihar Kaduna kan wasu tuhume-tuhume takwas
  • Ana zargin jiga-jigan jami'ar biyu da wawure kudin gyaran shahararriyar otel din Kongo da ke Zariya

Kaduna - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba a gaban Alkali A. A bello na babbar kotun jihar Kaduna.

EFCC ta gurfanar da Farfesa Garba ne tare da ma'ajin jami'ar, Ibrahim Shehu Usman, a yau Alhamis, 12 ga watan Janairu, jan wasu tuhume-tuhume takwas.

Tsohon shugaban ABU da ma'ajin jami'ar
An Gurfanar da Tsohon Shugaban ABU Da Ma'ajin Jami'ar Kan Zargin Damfarar N1bn Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Ana zarginsu da wawure fiye da naira biliyan daya

Hukumar ta EFCC reshen Kaduna na dai zargin jiga-jigan jami'ar biyu da aikata sata da wawure kudade da yawansu ya fi naira biliyan daya.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Ainihin Manufar Ƙirƙirar Ƙungiyar Boko Haram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gurfanar da su ne bayan shafe tsawon watanni ana bincike a kan wata kara da ke zargin mutanen biyu da karkatar da kudin da aka ware don aikin gyaran shahararriyar dakin taron nan na otel din Kongo da ke Zariya.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Twitter, ta ce binciken ya nuna cewa wadanda ake karar sun sace fiye da naira biliyan daya daga asusun jami'ar sannan suka karkatar da su zuwa nasu asusun bankin.

Matasa sun shiga hannu bayan sun sace yarinya yar shekara 6 a Kano

A wani labari na daban, rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kamun wasu matasa masu shekaru 19 su uku kan zarginsu da ake yi da sace wata yarinya yar shekara shida.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Yi Kicibus Da Muggan Makamai a Hannun Wata Mata Da Namiji a Jihar Arewa

Bayan sun sace yarinyar a jihar Kano, wadanda ake zargin sun dauke ta zuwa jihar Katsina sannan suka bukaci iyayenta da su biya kudin fansarta naira miliyan biyu.

A wajen karbar kudin fansar ne yan sanda suka yi nasarar cafke daya daga cikinsu mai suna Aliyu Salisu wanda a yayin bincike ne aka gano sauran sannan kuma an ceto yarinyar mai suna Fatima Abubakar cikin koshin lafiya. Za a gurfanar da su a kotu bayan bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel