Dalilin da Yasa Nayi Karyar Anyi Garkuwa Da Ni Don Mabiya Su Biya Fansa, Fasto

Dalilin da Yasa Nayi Karyar Anyi Garkuwa Da Ni Don Mabiya Su Biya Fansa, Fasto

  • Babban faston cocin ECWA ya ce ayi hakuri ya yi nadamar karyar da ya yiwa mabiyansa ya karbi kudi
  • Fasto Bitrus ya ce bukatar kudi ya jefashi cikin halin da ya shiga amma ayi hakuri ba zai sake ba
  • Faston ya yi karyar an yi garkuwa da shi har sau biyu kuma ya karbi kudi Naira dubu dari shida

Jos - Wani Fasto dan jihar Jos, Bitrus Albarka, wanda aka kama ranar Laraba kan zargin yin garkuwa da kansa ya bayyanawa yan sanda dalilin da ya sa yayi hakan.

Bitrus yace ya shirya hakan ne domin samun kudin biyan wasu bukatunsa.

Hukumar yan sandan jihar ta ce bincike ya nuna cewa Fasto Albarka na cocin ECWA ya hada bai da wasu don sace shi sannan su karbi kudin fansa, rahoton PremiumTimes.

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

Yayin bayyanashi ga manema labarai ranar Alhamis, faston ya yi nadamar abin da yayi.

Yace:

"Na cusa kaina cikin harkokin nan ne saboda ina fama da wasu matsaloli na kudi. Da nayi na farko na tsargu. Lokacin da na fita kudin suka kare. Sai na sake yi. Ina nadamar abinda nayi."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Gaba daya na rikice. Ban san abinda ya hau kaina ba. A matsayina na fasto, ina mai bada hakuri bisa abinda na aikata. Ayi hakuri."
Bitrus
Dalilin da Yasa Nayi Karyar Anyi Garkuwa Da Ni Don Mabiya Su Biya Fansa, Fasto Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Hukumar yan sandan jihar a jawabin da ta fitar ta ce faston ya karbin kudi N400,000 ranar 14 ga Nuwamba, 2022, sannan kuma a ranar 30 ga Nuwamba ya sake shirya garkuwa da hakkan kuma ya karbi N200,000 wajen mambobin cocinsa, riwayar Tribune.

A cewar jawabin:

"Ya shirya saceshi na karya ranar 14/11/2022 da 30/11/2022 inda mabiyansa suna biya Dubu dari hudu (N400,000) da Dubu dari biyu (N200,000), hakan yasa aka fara zarginsa."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

"Yayinda bincike, mutumin ya amince da aikata laifun kuma ya ambaci sunayen wadanda suka aikata tare: (1) Baruk Mailale, (2) Nathaniel Bitrus sukkan yan garin Yelwan Zangam da karamar hukumar Jos North da kuma Aye, wani dan Jalingo a Taraba."

Hukumar ta kara da cewa jami'anta na Nasarawa Gwong, Jos North sun damke mutum biyu cikinsu (1) Baruk Mailale, (2) Nathaniel Bitrus yayinda ake kan neman Aye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel