Latest
Gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na yin gwanjon kamfanonin rarraba wutar lantarki na Abuja, Benin, Kaduna, Kano da Ibadan sakamakon rashin wadatuwar wuta.
Kungiyar raya al'adun karamar hukumar Bokkos a jihar Filato ta yi tit da kisan da wani soja ya yi a yankin yayin da yake bikin ƙarin shekara ranar Litinin.
Akalla 'yan bindiga bakwai ne suka ajiye makaman su tare da mika wuya ga gwamnatin jihar Filato bayan zaman sulhu. An ruwaito su ne ke addabar garuruwan Wase.
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ba Shugaban Bola Tinubu shawara kan sanya daliban Jami'o'i cikin tsarin lamunin ɗalibai da aka kirkira.
Kotun zaɓe ta kammala zaman sauraron hujjojin kowane ɓangare a karar da ɗan takarar APC ya ƙalubalanci nasarar Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa.
Ministan Ilimi ya bayyana adadin daliban da za su samu guraben karatu a manyan makarantun kasar nan. Ya ce kaso ashirin cikin dari na wadanda su ka zauna UTME ne
Sakamakon ta'adin da wasu bata gari da suka yi na lalata hasumiyoyin da suke dauke da layukan wutar lantarki a hanyar Jos, jihohi uku sun shiga duhu a Arewa.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa zai kafa kamfanin siminti a jihar Gombe. Ya kuma yi bayanin dalilai da ya zabi jihar da yadda kamfanin zai kawo saukin farashi
Yayin da 'yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, farashin iskar gas ya sake tashi yayin da ya bambanta a jihohin Najeriya daban-daban inda wasu ke siya da sauƙi.
Masu zafi
Samu kari