TCN: Ana Kokarin Gyara Wutar Lantarki Bayan Jihohi 3 Sun Shiga Cikin Duhu

TCN: Ana Kokarin Gyara Wutar Lantarki Bayan Jihohi 3 Sun Shiga Cikin Duhu

  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya tabbatar da cewa jihohin Adamawa, Gombe da Taraba sun shiga cikin duhu
  • Wannan kuwa a cewar TCN ya faru ne sakamakon lalata hasumiya guda hudu da ke rarraba wutar lantarki a hanyar Jos-Gombe
  • Kamfanin ya ce zai yi duk mai yiwuwa don gyara wutar yankunan da abin ya shafa yayin da ake kokarin tada hasumiyoyin da aka lalata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN), ya tabbatar da cewa bata gari sun lalata hasumiya guda hudu da ke rarraba wutar lantarki a hanyar Jos-Gombe.

Bata gari sun lalata hasumiyoyin da suka kai wutar lantarki jihohi uku a Arewa
Gombe, Adamawa da Taraba sun shiga duhu sakamakon lalata hasumiyar wutar lantarki. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jihihohi 3 da za su shiga duhu

Lalata hasumiyar layukan wutar ya janyo an fada cikin rashin wutar lantarki a jihohi uku da suka hada da Adamawa, Gombe da Taraba.

Kara karanta wannan

Filato: Soja da ke shagalin ƙara shekara ya bindige wani bawan Allah har lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta ruwaito manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Litinin.

Sakamakon haka, wutar lantarki a tashoshin Gombe, Yola, da Jalingo ta lalace, lamarin da ya yi illa ga yawan wutar lantarkin da kamfanonin rarraba wutar na Yola da Jos ke samu.

"An lalata husumiyoyi 4" - TCN

“Kamfanin TCN yana sanar da cewa an lalata hasumiyoyi hudu da ke dauke da manyan layukan rarraba wutar lantarki ta hanyar Jos zuwa Gombe mai karfin kilo 330kV da misalin karfe 3:32 na yammacin yau 22 ga Afrilu, 2024.
“A yayin wani rangadi ne injiniyoyin TCN suka gano cewa an lalata hasumiya ta 288, 289, 290, da 291 kuma an datse layukan wasu hasumiyoyin, wannan tasa sun daina aiki gaba daya.

Kara karanta wannan

An ɗauke wuta a jihohin Arewa 3 yayin da tsageru suka lalata wayoyin lantarki

"A yanzu haka wutar lantarki a tashoshin Gombe, Yola, da Jalingo ta lalace, lamarin da ya yi illa ga yawan wutar lantarkin da kamfanonin rarraba wutar na Yola da Jos ke samu."

- Ndidi Mbah.

TCN na kokarin gyara wutar Gombe

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, TCN ya ce yana kokarin dawo da wutar Gombe ta hanyar amfani da tashar wutar mai karfin 132kV daga Bauchi.

Haka kuma akwai shirin dawo da wutar Ashaka, Potiskum, Damaturu, da Billiri/Savannah bayan an gyara ta gombe.

"Za mu yi duk mai yiwuwa don maido da wutar a yankunan da abin ya shafa yayin da ake kokarin sake hada hasumiyai hudu da aka lalata."

- In ji sanarwar.

Idan ba a manta ba an jefa Abuja cikin duhu a watan Fabrairu saboda barnar da wasu bata gari suka yi wa hasumiyar TCN.

An yi awanni 10 babu wuta a Gombe

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa lalacewar hasumiyoyin wutar lantarki na kamfanin TCN ya jawo Gombe ta fada a duhu na tsawon awanni 10.

Amma sabanin rahoton TCN na cewa bata gari ne suka lalata hasumiyoyin, hukumar kamfanin rarraba wutar ta Jos a ranar Litinin ta ce iska da ruwan sama suka jawo matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel