Aliko Dangote Zai Gina Wani Sabon Kamfanin Siminti a Arewacin Najeriya

Aliko Dangote Zai Gina Wani Sabon Kamfanin Siminti a Arewacin Najeriya

  • Wanda ya fi kowa arziki a Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya yi alkawarin kafa sabon kamfanin siminti a jihar Gombe
  • Ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jarida jim kaɗan bayan ganawar sirri da ya yi da gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya
  • Legit ta tattauna da wani mai harkar siminti a jihar Gombe, Muhammad Babari, kuma ya nuna shakku kan kudurin na Dangote

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Shahararren dan kasuwa kuma mai arzikin Afrika na daya, Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin gina kamfanin siminti a jihar Gombe.

Dangote
Dangote ya ce zai kafa kamfanin siminti a Gombe Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

Alhaji Aliko Dangote ya bayyana haka ne yayin bikin auren 'yar Alhaji Umaru Kwairanga a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

Dalilin Dangote na kafa kamfani a Gombe

Mai taimakawa gwamnan jihar Gombe a harkar yada labarai, Isma'ila Uba Misilli ya fitar da sanarwa a shafinsa na Facebook cewa Dangote ya ce zai kafa kamfanin ne lura da yadda al'amuran kasuwanci ke bunkasa a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara kuma da cewa gwamnan jihar ya samar da yanayi mai kyau da zai taimakawa kasuwanci wurin habaka da kuma irin yadda jihar ke da sinadarin hada siminti sosai.

Yadda Dangote zai kawo saukar farashi

Dangote ya tabbatar da cewa idan suka fara hada siminti a jihar Gombe akwai yiwuwar farashin siminti zai sauka a yankunan da su ke kewaye da Gombe.

Za a samu wannan rangwame ne saboda rage nisan jigilar simintin da za a samu.

Shakku kan kafa kamfanin siminti a Gombe

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80

A hirar da Legit ta yi da Muhammad Babari, wani mai harkar siminti a jihar Gombe, ya nuna shakku a kan yiwuwar kafa kamfanin simintin Dangote.

Ya ce duk da kuduri ne mai kyau amma da wahala hakan ya tabbata. Saboda a cewarsa, akwai Madugu Cement da suka zo da irin wannan kudiri, har samfura sun nuna amma kuma abin ya gagara.

Babari ya ce abin da yake hana cimma irin wannan kudirin yawanci sabanin siyasa ne kamar yadda ya faru da kamfanin Ibeto a Ado-Ekiti.

A kan maganar sauke farashi kuma, ya ce lalle za a iya gaskata Dangote saboda koda a yanzu shine babban mai fada a ji a harkar siminti a Najeriya. Da zarar ya saukar da farashi to sauran kamfanoni ma za su saukar.

An dawo da dokar shara a Gombe

A wani rahoton kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta sanar da dokar sharar gama gari da za a rika yi duk ranar Asabar din karshen wata a fadin jihar

Kara karanta wannan

Ganduje: An sake bankado yadda tsohon gwamnan ya karkatar da N51.3bn, an gano dalili

Dokar zata fara aiki ne a karshen watan Afrilu kuma za a rika daukan awa biyu ana gudanar da ita ba tare da barin zirga-zirgar al'umma ba

Gwamnatin ta yi kira ga daukacin al'ummar jihar da su yi iya kokari wurin bada hadin kai ga hukumomi domin tabbatar da tsaftace jihar baki daya

Asali: Legit.ng

Online view pixel