Gwamnati Za Ta Yi Gwanjon Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki 5, Abubuwa Sun Lalace

Gwamnati Za Ta Yi Gwanjon Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki 5, Abubuwa Sun Lalace

  • Sakamakon karancin wuta a Najeriya, gwamnati ta ce za ta sayar da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) guda biyar na kasar
  • Gwamnatin tarayya ta ce bankuna da kamfanin AMCON ba su da karfin fasahar tafiyar da kamfanonin rarraba wutar lantarki
  • Haka zalika ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu ya ce gwamnati ta soke kwangilar samar da mitoci ta Dala miliyan 200

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja -A jiya ne gwamnatin tarayya ta sha alwashin sayar da kamfanonin rarraba wutar lantarki guda biyar (DisCos) yayin da ake ci gaba da rashin wuta a kasar.

Gwamnati za ta cefanar da kamfanonin rarraba lantarki guda 5
Gwamnati za ta yi gwanjon kamfanonin lantarki na Abuja, Benin, Kaduna, Kano da Ibadan. Hoto: @BayoAdelabu
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayya ta kuma soke kwangilar samar da mitoci ta Dala miliyan 200 da ta bayar tun a 2021 amma aka gaza aiwatarwa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

TCN: Ana kokarin gyara wutar lantarki bayan jihohi 3 sun shiga cikin Duhu

Gwamnati ta sutale bankuna da AMCON

A baya ne bankuna da kamfanin kula da kaddarori (AMCON), suka karbi ragamar kula da wadannan DisCos din saboda gazawar hukumomin wajen biyan basussuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu ya ce bankuna da AMCON ba su da karfin fasahar tafiyar da kamfanonin rarraba wutar.

Adelabu ya kara da cewa ana sa ran kammala siyar da manyan kamfanonin samar da wutar lantarki a cikin watanni uku ga wadanda aka san suna da karfin kula da su.

Kamfanonin wutan da za a yi gwanjon su

  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC)
  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na Benin (BEDC)
  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna
  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano
  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IEDC)

DisCos sun fadi dalilin rashin wuta

Kara karanta wannan

Hukumar FCCPC ta rufe kantin da ya hana 'yan Najeriya sayayya a Abuja

Jaridar Premium Times ruwaito cewa masu zuba jari suna ke rike da kashi 60% na hannun jari a cikin kamfanonin yayin da gwamnatin tarayya ke rike da kashi 40%.

Ana ci gaba da samun matsalar wutar lantarki a yawancin jihohi tare inda kamfanonin DisCos ke alakanta hakan daga ƙarancin kason wutar daga tashar wutar ta ƙasa

Haka kuma sun alakanta rashin wutar da ƙarancin iskar gas ga kamfanoni masu samar da wutar (GenCos) a da da sauran dalilai.

Jihohi 3 sun fada cikin duhu

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa bata gari sun lalata hasumiyoyin wutar lantarki a hanyar Jos.

A cewar TCN wannan ya jawo daukewar wuta a jihohin Adamawa, Gombe da Taraba, yayin da ya ce yanzu yana kokarin gyara wutar Gombe ta hanyar amfani da tashar lantarki ta Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel